Labarai
Tsaftar Muhalli: An Bukaci Shugabannin Su Yi Koyi da Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kudu
Daga Usman Muhammad Zaria
An bayyana rashin tsaftar muhalli a matsayin babbar hanyar haddasa matsalolin lafiya a cikin al’umma.
Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kudu, Dokta Builder Muhammad Uba, ya bayyana hakan a yayin aikin tsaftar muhalli na kowane wata da aka gudanar a Birnin Kudu.

Shugaban ya sake jaddada jajircewarsa wajen tabbatar da tsaftar muhalli ta hanyar halartar aikin tsaftar muhalli na karshen wata, wanda ake gudanarwa a duk ranar Asabar ta karshe ta kowane wata.
Dokta Muhammad Uba, ya jaddada muhimmancin tsaftar muhalli tare da kira ga al’ummar yankin da su rika tsaftace muhallinsu a kowane lokaci.

Ya bayyana cewa kula da tsaftar muhalli hakki ne da ya rataya a wuyan kowa da kowa domin samar da muhalli mai tsafta da lafiya.
Haka kuma, ya tabbatar wa al’umma cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da ba da goyon baya ga shirye-shiryen da ke inganta tsaftar muhalli da kula da lafiyar jama’a.

Builder ya kuma bukaci mazauna yankin da su dauki alhakin kula da muhallinsu tare da yin aiki tukuru domin tsaftace Karamar Hukumar ta Birnin Kudu.
Rediyon Najeriya ya ruwaito cewa an gudanar da atisayen tsaftar muhalli na kowane wata a wuraren taruwar jama’a, kasuwanni da unguwanni, inda mahalarta suka bukaci masu ruwa da tsaki su yi koyi da kyakkyawan jagorancin Shugaban Karamar Hukumar tare da ba da fifiko ga tsaftar muhalli.

-
Labarai6 days agoRamadan: Sarkin Kauru Ya Bukaci a Kara Karfafa Tsaro Tare da Tallafawa Marasa Galihu
-
Labarai5 days agoKaramar Hukumar Birnin Kudu ta Nemi Hadin Kan Kungiyar ‘Yan Achaba Wajen Dakile Matsalar Tsaro
-
Labarai5 days agoSojojin Najeriya Sun Karɓi Motocin Yakin Da Aka Kera A Cikin Ƙasa
-
Labarai5 days agoMajalisar Dokokin Jihar Kano Ta Fara Shari’ar Tsige Mataimakin Gwamna Aminu Abdulsalam
-
Labarai2 days agoRanar Mata Ta Duniya: Gwamnatin Kano Ta Bukaci A Kara Tallafa wa Mata da ’Yan Mata
-
Labarai5 days agoTsarin Kundin Shirin Bunkasa Samarda Abinci Mai Gina Jiki
-
Labarai6 days agoKungiyoyin Alumma a Jigawa Sun Bayyana Goyon Bayansu ga Gwamna Namadi Kan Lamarin Walida Abdulhadi
-
Labarai4 days agoGwamnatin Zamfara Ta Ayana Dokar Ta-baci Kan Shan-Inna a Karamar Hukumar Gummi
