Connect with us

Ilimi

Jami’ar Tarayya Dutse Za ta Rantsar da Sabon Shugabanta Ranar 10 ga Watan Fabrairu

Published

on

Daga Usman Muhammad Zaria

Jami’ar Tarayya ta Dutse (FUD) ta bayyana cewa za a rantsar da sabon Shugaban Jami’ar (Vice-Chancellor) da aka naɗa, Farfesa Ahmad Muhammed Gumel, zai gudana a ranar Talata, 10 ga watan Fabrairun 2026 kamar yadda aka tsara.

Lauyan mai kare wadanda ake kara, Barrista Shamsu Ubale Jibrin ne ya sanar da hakan ga manema labarai a Dutse,  babban birnin jihar.

Hakan na zuwa ne  bayan ƙarar da Farfesa Abdulsalam Balarabe, ɗaya daga cikin masu neman kujerar Shugaban Jami’ar, ya shigar ta hannun lauyansa, inda yake ƙalubalantar tsarin zaɓen tare da roƙon kotu da ta hana Majalisar Gudanarwa da sauran waɗanda ake ƙara a shari’ar gudanar da bikin rantsarwar da miƙa mulki ga sabon Shugaban Jami’ar.

Barrista Jibrin ya ce a gabatarwarsa, ya gabatar da hujjoji masu ƙarfi tare da takardun shaidar gaskiya a gaban kotu, waɗanda ke nuna cewa an kammala tsarin zaɓen cikin tsari ba tare da karya daya daga cikin ƙa’idojin cancanta da aka ayyana a tallar da aka wallafa a jaridun ƙasa ba.

Ya ƙara da cewa lauyan Farfesa Abdulsalam Salam ya kasa gabatar da wata hujja a gaban kotu da za ta nuna cewa ba a bi ka’ida ba wajen naɗa sabon  Shugaban Jami’ar.

Ya ce daga hujjojin da ya gabatar a gaban kotu, Farfesa Gumel ya cika dukkan sharuddan da ake buƙata don naɗa shi a matsayin Shugaban Jami’a, inda ya samu maki mafi yawa, tare da zama na farko a tantancewar da aka yi wa ‘yan takarar, sannan Majalisar Gudanarwa cikin hikimarta ta naɗa shi a matsayin  Shugaban Jami’ar na huɗu.

Ya ce kotu ba ta amince da roƙon dakatar da rantsarwar ba, sai dai cikin hikimarta ta ɗage sauraron shari’ar zuwa 23 ga Fabrairu bayan an kammala bikin rantsarwar.

A cewarsa, wannan wata nasara ce ga  Majalisar Gudanarwa da Farfesa Gumel.

Barrista Jibrin ya bayyana cewa ya gabatar da hujjoji ingantattu don tabbatar da cewa Farfesa Gumel ya cika sharadin ƙwarewar aiki na shekaru 15 a jami’a a zaman kotu da aka gudanar a ranar Alhamis.

 

 

Labarai

Ilimi1 day ago

KANO: Ungogo Ta Ƙaddamar da Shirin Shigar da Yara Makaranta

Daga Khadijah Aliyu Ƙaramar Hukumar Ungogo ta Jihar Kano ta ƙaddamar da wani shirin wayar da kan jama’a domin shigar...

Labarai1 day ago

Jihar Naija Ta Dauki Matakan Gaggawa Sakamakon Bullar Cutar Ebola A Abuja

Daga Aliyu Lawal Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Nijar ta sanya Cibiyar Ayyukan Gaggawa ta Lafiyar Jama’a (PHEOC) cikin shirin ko-ta-kwana,...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Tarayya Ta Ɗauki Matakan Gaggawa Bayan Tabbatar da Ebola a Birnin Tarayya

Daga Bello Wakili  Gwamnatin Tarayya ta fara aiwatar da matakan gaggawa na kare lafiyar jama’a,  bayan tabbatar da bullar cutar...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Amince Da Fitar Da Naira Biliyan 1.4 Ga Mazabu

Daga Usman Muhammad  Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da kashe sama da naira biliyan 1.4 wajen aiwatar da ayyukan mazabu...

Fasaha2 days ago

Jigawa Ta Ware Naira Miliyan 380 Don Samar da Wutar Lantarki a Cibiyoyin ICT

Daga Usman Muhammad Zaria  Majalisar Zartarwa ta Jihar Jigawa ta amince da kashe sama da naira miliyan 380 wajen samarwa...

Labarai2 days ago

’Yan Sanda Sun Kama Wanda Ake Zargi da Fashi da Makami A Kano

Daga ABDULLAHI JALALUDDEEN, KANO Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta kama wani mutum da ake zargi da aikata fashi da...

Labarai2 days ago

2027: Ombugadu Ya Yi Alƙawarin kawo Ƙarshen Rashin Tsaro

Daga ALIYU MURAKI, LAFIA Ɗan takara a zaɓen gwamnan Jihar Nasarawa na jam’iyyar PDP, Dr. Emmanuel Ombugadu, ya yi alƙawarin...

Labarai2 days ago

Tajudeen Zai Bayyana Rahoton Ayyukan Tinubu Cikin Kwanaki 14

Daga BELLO WAKILI, Abuja Shugaban Majalisar Wakilai ta Najeriya, Dr. Abbas Tajudeen, ya ce zai bayyana cikakken rahoton nasarorin da...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Zamfara Ta Nuna Damuwa Kan Ƙaruwar Hare-Haren ’Yan Bindiga

Daga AMINU DALHATU Gwamnatin Jihar Zamfara ta bayyana matuƙar damuwarta kan ƙaruwar hare-haren ’yan bindiga a wasu sassan jihar a...

Kasuwanci2 days ago

APC Ta Ce Kebbi Na Tare da Tinubu Dari-bisa-Dari

Daga SANI DUTSINMA Babban Daraktan Yaƙin Neman Zaɓen ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC, Sanata Abdulazeez Yari, ya ce...

Mafi Shahara