Ilimi
An Sace Ɗalibai 1,683 a Makarantu cikin Shekaru 8 – Rahoto
Aƙalla yara da ɗalibai 1,683 ne aka sace a makarantu a Najeriya tsakanin shekarun 2014 zuwa 2022, sakamakon hare-haren da ƙungiyoyin ’yan bindiga da masu tayar da ƙayar baya suka kai makarantu har sau 70 a cikin wannan lokaci.
Wani rahoto da ƙungiyar agaji ta ƙasa da ƙasa, Save the Children International (SCI), ta fitar domin bikin Ranar Ilimi ta Duniya ta 2026, ya kuma bayyana cewa ɗalibai 184 sun rasa rayukansu a yayin waɗannan hare-hare, yayin da gine-ginen makarantu 25 suka lalace.
Rahoton, wanda aka miƙa wa ’yan jarida a Jihar Katsina, ya nuna cewa rikicin ya fi muni a jihohin Arewa maso Gabas da Arewa maso Yamma, inda hare-haren makarantu, sace-sacen jama’a gaba ɗaya, da ƙauracewar al’umma ke ci gaba da yawaita. Wannan na hana ƙoƙarin gwamnati da abokan hulɗa na inganta ingancin ilimi samun nasara.
Rahoton ya gargaɗi cewa, “ba tare da tabbatar da tsaron makarantu da kuma samar da isasshen kuɗaɗen da za a zuba a ɓangaren ilimi ba, ƙwarewa da baiwar matasan Najeriya—waɗanda suka haura kashi 60 cikin 100 na yawan al’umma—za su ci gaba da kasancewa a takure.”
Haka kuma, rahoton ya yi kira da a aiwatar da Dokar Kare Tsaron gaba ɗaya, tare da ɗaukar tsauraran matakan tsaro don kare yara a wuraren koyonsu. Ya bayyana matasa a matsayin “ba shugabannin gobe kaɗai ba, har ma manyan ginshiƙan sauyi a yau.”
Rahoton ya ƙara da cewa ƙungiyar na ci gaba da jajircewa wajen ƙarfafa fafutukar matasa domin ganin an aiwatar da Shirin Kare Makarantu, tallafawa ilimi a lokutan gaggawa, da bunƙasa basira da ƙwarewar matasa da rikice-rikice da ƙauracewa suka shafa.
Isma’il Adamu
-
Labarai4 days agoHukumar Alhazai Ta Jigawa Ta Bayyana Alhininta Bisa Rasuwar Suleiman Usman
-
Fasaha3 days agoNASENI Ta Ƙarfafa Horar da Sana’o’i da Fasahar Jiragen Sama Marasa Matuki a Kaduna
-
Labarai3 days agoNSCDC Ta Kama Wanda Ake Zargi Da Safarar Mutane A Zamfara
-
Labarai2 days agoGwamnatin Tarayya Ta Ɗauki Matakan Gaggawa Bayan Tabbatar da Ebola a Birnin Tarayya
-
Labarai2 days agoGwamna Uba Sani Ya Ce Bunƙasa Ƙwarewa Na Da Muhimmanci Ga Farfaɗo Da Tattalin Arziki
-
Labarai2 days agoGwamnatin Zamfara Ta Nuna Damuwa Kan Ƙaruwar Hare-Haren ’Yan Bindiga
-
Labarai2 days agoTajudeen Zai Bayyana Rahoton Ayyukan Tinubu Cikin Kwanaki 14
-
Labarai2 days ago2027: Ombugadu Ya Yi Alƙawarin kawo Ƙarshen Rashin Tsaro
