Labarai
An Tsinci Gawar Wani Mutum A Cikin Rijiya A Karamar Hukumar Gezawa
Al’ummar kauyen Babawa da ke karamar hukumar Gezawa a Kano sun shiga cikin firgici bayan da aka tsinci wani mutum mai kimanin shekaru 45 a cikin rijiya.
Saminu Yusif Abdullahi jami’in hulda da jama’a na hukumar kashe gobara ta jihar Kano ya tabbatarwa manema labarai faruwar lamarin.
Ya bayyana cewa hukumar ta samu kiran gaggawa daga ASP Kabiru Lawan na rundunar ‘yan sandan Gezawa.
Saminu ya yi nuni da cewa, tawagar ceto ta yi nasarar zakulo mutumin daga rijiyar kuma daga bisani jami’an lafiya suka tabbatar da mutuwarsa.
Sai dai, ya jaddada cewa, har yanzu ba a san ko wanen ba, saboda shugabannin al’umma da mazauna yankin sun ce ba su gane shi ba, ba su kuma san daga inda ya fito ba.
Hakazalika, mutane uku sun makale a lokacin da suke aikin hako rijiya a kauyen Gargajiga da ke karamar hukumar Minjibir.
Saminu ya kara da cewa hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta ceto mutum biyu da ransu, yayin da aka dauko mutum na uku Yusuf Nadabo mai shekaru 50 da haihuwa, a sume, daga bisani kuma aka tabbatar da mutuwarsa.
Jami’in hulda da jama’an ya yi nuni da cewa, wani iftila’in ya sake afkuwa a Kano inda wata mummunar gobara ta kona shaguna da dama a kan titin Ibrahim Taiwo, inda aka ciro wani mutum a sume, yayin da aka yi asarar dukiyoyi na miliyoyin naira.
Daga Khadija Aliyu
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
