Connect with us

Labarai

Gwamnatin Jigawa Za Ta Bada Lamunin Sama Da Naira Biliyan 3 Ga Hukumar Alhazan Jihar

Published

on

Majalisar zartaswa ta jihar Jigawa ta amince da bukatar hukumar Alhazai ta jihar na naira biliyan uku da miliyan dari uku da sittin a matsayin lamuni daga gwamnatin jihar.

Kwamishinan yada labarai, matasa, wasanni da al’adu na jihar Alhaji Sagir Musa Ahmed ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai, bayan kammala taron majalisar da aka gudanar a gidan gwamnati dake Dutse.

Ya bayyana cewa,  majalisar ta amince da hakan ne don bai wa hukumar damar ajiyar kujeru 400 na maniyyatan jihar Jigawa domin gudanar da ayyukin  Hajjin shekarar 2025.

A cewarsa, amincewar ta biyo bayan  gamsuwar da Majalisar ta yi, bisa yadda hukumar Alhazai ta Jiha ta mayar da bashin Naira biliyan biyu da miliyan dari biyu da gwamnatin ta bata a shekarar 2024.

Haka zalika Alhaji Sagir Musa Ahmed ya ce majalisar ta amince da shigar da dukkan masu rike da mukaman siyasa a cikin shirin kula da liyafa na jihar, kamar yadda hukumar kula da lafiya ta jihar Jigawa  JICHMA ta tanadar  a doka mai lamba. 02 -2024, da nufin inganta harkokin kiwon lafiya a jihar da ma Najeriya baki daya kamar yadda sakataren gwamnatin jihar ya gabatar.

Ya ce majalisar ta kuma bada goyon baya ga amincewar da Gwamna Umar Namadi ya yi, na sakin Naira Miliyan Dari Biyu da Hamsin a matsayin wani asusun hadin gwiwa da hukumar UNICEF domin siyan kayan abinci mai gina jiki ga kananan yara marasa lafiya.

Ya kara da cewa, amincewar kuma wani bangare ne na kokarin gwamnatin Namadi na yaki da matsalar rashin abinci mai gina jiki a tsakanin yara a jihar, kamar yadda ma’aikatar lafiya ta gabatar.

 

Usman Muhammad Zaria

Labarai

Labarai4 hours ago

Hajjin 2026: Jigawa Ta Kaddamar da Tawagar Likitoci da Za Su Kula Da Alhazai

Usman Mohammed Zaria Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Jigawa ta kaddamar da tawagar likitoci domin kula da lafiya da...

Labarai4 days ago

Matasan Kauru Sun Yi Allah-wadai da Mulkin Ƙarfi, Sun Buƙaci Adalci da Haɗin Kai

  Daga Yusuf Zubairu Wata ƙungiyar matasa a Ƙaramar Hukumar Kauru ta Jihar Kaduna ta bayyana cewa shugabanci na bai-ɗaya...

Labarai5 days ago

Ma’aikatar Lafiya Ta Fara Daukar Jami’an Kula da Lafiya na Ƙasa a Jigawa

Usman Muhammad Zaria  Ma’aikatar Lafiya ta kasa karkashin shirin kula da lafiya na SWAP ta fara aikin daukar Jami’an Kula...

Labarai2 weeks ago

Baragurbi a Aikin Jarida na Barazana ga Sahihancin Kafafen Yada Labarai – Shugaban NUJ-FRCN

Shugaban Ƙungiyar ’Yan Jarida ta Najeriya (NUJ), reshen FRCN Kaduna, Kwamared Umar Adamu Sarkinfada, ya bayyana cewa mummunan aikin jarida...

Labarai2 weeks ago

Ƙaruwa a Shan Abubuwan Sha Masu Ƙara Ƙarfi na Haddasa Damuwar Lafiya a Kano

Abubuwan sha masu ƙara ƙarfi, waɗanda aka fi sani da energy drinks ko energizers, na ƙara samun karɓuwa a faɗin...

Labarai2 weeks ago

Shugaba Tinubu Ya Taya CPSO Usman Shugaba Murnar Cika Shekara 45 da Haihuwa

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya Kwamishinan ‘Yan Sanda, Usman Musa Shugaba, wanda shi ne Babban Jami’in Tsaron ‘Yan...

Labarai2 weeks ago

TSARO: Gwamnan Jihar Neja Ya Nuna Alhini Kan Harin ‘Yan Ta’adda a Al’ummomin Borgu

Gwamnan Jihar Neja, Mohammed Umar Bago, ya bayyana matuƙar baƙin cikinsa kan harin ‘yan ta’adda da aka kai wa wasu...

Labarai2 weeks ago

Allah Ya Jikan Jarman Kauru Da Ke Jihar Kaduna

Mun sami labarin rasuwar tsohon Kwamishinan Ilimi na Jihar Kaduna, Malam Suleiman Lawal Jarman Kauru. Malam Suleiman Lawal, mai shekaru...

Labarai3 weeks ago

Gwamnatin Kano Ta Faɗaɗa Damar Tattalin Arziki ga Mata da Masu Buƙata Ta Musamman

An kammala kasuwar baje kolin mata ta tsawon kwanaki huɗu, wadda Ma’aikatar Harkokin Mata, Yara da Masu Buƙata Ta Musamman...

Labarai3 weeks ago

Rundunar Tsaro Ta Haɗin Gwiwa Ta Hallaka ’Yan Bindiga 150

Rundunar tsaro ta haɗin gwiwa da ta ƙunshi Sojojin Nijeriya, Hukumar Tsaron Farin Ciki (DSS), ’Yan Sanda da sauran hukumomin...

Mafi Shahara