Connect with us

Labarai

CAN Ta Yaba Saboda Agajin Gaggawa Ga Mutanen Da Fashewar Tanka Ta Shafa a Neja

Published

on

Kungiyar kiristocin Najeriya reshen jihar Neja (CCN) ta yaba da martanin gaggawar da gwamna Umar Mohamed Bago ya yi kan fashewar tankar da ta afku a mahadar Diko da ke karamar hukumar Gurara a jihar.

 

Shugaban karamar hukumar Daniel Tsado wanda ya yi wannan yabon a cikin wata sanarwa da ya fitar a Minna, ya ce saurin mayar da martanin da Gwamnan ya yi sa’o’i kadan bayan faruwar lamarin na nuna matukar damuwarsa kan halin da al’ummar jihar ke ciki.

 

Ya jajanta wa Gwamnatin Jihar Neja game da mutuwar da aka yi tare da bukatar wadanda suka rasa ‘yan uwansu da su dauki wannan rashi kaddara daga Ubangiji, yana mai cewa mutuwa za ta iya zuwa ta kowace hanya kuma a kowane hali.

 

Venerable Daniel Tsado wanda kuma shi ne Mataimakin Cocin St Peter’s Anglican na Gbaiko a karamar hukumar Bosso, ya yi addu’ar Allah ya jikan wadanda suka rasa rayukansu sakamakon fashewar a ranar Asabar.

 

Ya kuma yi bayanin cewa daukacin Coci-coci na jihar suna bakin ciki kan wannan mummunan lamari tare da jajanta wa Gwamnan Jihar Neja, Umar Bago kan rasuwar da aka samu.

 

Shugaban ya kuma tabbatar da kudurin CCN reshen jihar Neja na goyon bayansu ga manufofi da shirye-shiryen gwamnatin Gwamna Bago don cimma sabuwar ajandar Neja.

 

Ya kuma yabawa gwamnatin tarayya bisa matakin da ta dauka na daukar nauyin biyan kudaden jinya ga wadanda abin ya shafa da ke cikin mawuyacin hali da aka tura zuwa Abuja, baya ga matakin da ta dauka na kafa wani kwamiti mai karfi da zai binciki musabbabin faruwar lamarin.

Labarai

Labarai22 hours ago

Kano: Kotu Ta Umarci A Lalata Buhunan Fulawa Sama Da 400

Daga Khadijah Aliyu  Wata kotu a Jihar Kano ta bayar da umarnin lalata buhunan fulawa sama da 400 da suka...

Labarai2 days ago

Tinubu Ya Jaddada Ƙudurin Samar Da Ci Gaba A Jigawa

Daga Usman Muhammad Zaria  Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sake jaddada ƙudurin gwamnatinsa na ci gaba da aiwatar da...

Labarai2 days ago

Shugaban Gidan Talabijin Na Katsina Abba Zayyan Ya Yi Murabus

Daga Isma’il Adamu  Babban Manajan gidan talabijin na Jihar Katsina (KTTV), Abba Zayyan, ya miƙa takardar murabus daga muƙaminsa a...

Labarai2 days ago

Namadi Ya Miƙa Buƙatu Uku Ga Tinubu Kan Ci gaban JiharJigawa

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya bukaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya kai musu...

Labarai2 days ago

Arewa Za Ta Saka Wa Tinubu Da Ruwan Kuri’a A 2027- Yari

Daga Usman Muhammad Zaria  Daraktan Janar na Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa na APC, Sanata Abdulaziz Yari, ya ce...

Labarai2 days ago

Shettima Ya Bukaci ’Yan Najeriya Su Sake Zaben Tinubu A 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya bukaci ’yan Najeriya da su goyi bayan sake zaɓen Shugaba...

Labarai3 days ago

Jigawa Ta Amfana Da Ayyukan Gwamnatin Tinubu – Abdulaziz

Daga Usman Muhammad Zaria Babban Mataimaki na Musamman ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan harkokin yada labarai da wayar dan...

Labarai3 days ago

Majalisar Kano Za Ta Karɓi Kasafin Kuɗin Shekarar 2027

Daga Khadijah Aliyu  Majalisar Dokokin Jihar Kano na shirin karɓar daftarin kasafin kuɗin shekarar 2027 daga Gwamna Abba Kabir Yusuf...

Labarai4 days ago

Yankin Funtua Sun Yi Fitowar Farin Dango A Yakin Neman Zaɓe Na APC- Hamza Faskari

Daga Isma’il Adamu  An bayyana yakin neman zaben jam’iyyar APC a yankin Sanatan Funtua na Jihar Katsina a matsayin nasara,...

Labarai4 days ago

Namadi Ya Ƙaddamar Da Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen APC Na 2027

Daga Usman Muhammad Zaria Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya ce an haɗa kwamitocin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa...

Mafi Shahara