Kasuwanci
Wata Ta Kungiya Ta Bada Shawara Gwamnatin Tarayya Akan Karfafa Matasa
Kungiyar matan Jami’an Sojojin Najeriya ta yi kira ga gwamnatin tarayya da gwamnatocin Jihohi da su samar da ingantattun hanyoyin inganta rayuwar matasa ta hanyar koyon sana’o’i don inganta zamantakewa da tattalin arzikin kasa.
Shugabar runduna ta 8 ta sojojin Najeriya reshen kungiyar kuma uwargidan Kwamandan runduna ta 8 dake Sakkwato Mrs. Meg Indidi Ajose ta yi wannan roko ne a lokacin da take kaddamar da wata sabuwar cibiyar koyar da sana’o’i ta Kungiyar da ke Sakkwato.
Ta ce sake fasalin cibiyar koyar da sana’o’i na daga cikin kudirin Kungiyar su na ganin ta kara kaimi ga kokarin gwamnatin tarayya a yunkurin tabbatar da karfafa gwiwar matasa ta hanyar samun sana’o’i.
Shugaban NAOWA ta yi nuni da cewa, koyon sana’o’in matasa na da matukar muhimmanci ga zaman lafiyar al’umma da ci gaban tattalin arzikin kasar.
Ta yi nuni da cewa, karfafa wa matasa sana’o’in da suka dace na tabbatar da dogaro da kai, da inganta harkokin kasuwanci da kuma ciyar da ci gaban fasaha a kasar nan.
Ta jaddada cewa saka hannun jari a kan matasa na taimakawa bunkasa zamantakewa da tattalin arziki da tsaro a kasar.
Rediyon Najeriya ya ruwaito cewa a yanzu haka ‘yan mata kimanin dari da goma sha shida ne ke samun horo kan sana’o’i daban-daban tun daga sana’ar dinki, sana’o’in hannu da gyaran gashi da dai sauransu.
Ita ma da take magana ko’odineta ta shiyyar Mrs Anne Omoh Tawasimi ta hori wadanda aka horas da su don cin gajiyar wannan dama tare da sadaukar da kansu kan wannan horon da nufin cimma burin da ake so.
NASIR MALALI/Wababe
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
