Connect with us

Labarai

Hukumar Alhazai Ta Jihar Jigawa Ta Samar Da Masauki Na Alfarma Ga Alhazan Jihar

Published

on

Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Jigawa ta ce ta samar wa Alhazan Jiha katafaren masauki na alfarma  a kusa da Harami da ke Makkah.

Babban Daraktan hukumar Alhaji Ahmed Umar Labbo ne ya bayyana hakan ga wakilin gidan rediyon Najeriya a Dutse babban birnin jihar.

Ya ce hukumar ta samar da masauki na alfarma kusa da masallacin Harami, domin baiwa Alhazan jihar damar ziyartar babban masallacin ba tare da wahala ba.

Ya kuma bayyana cewa, Gwamna Umar Namadi a shirye yake ya ba hukumar tallafin da ya dace domin tabbatar da ganin Alhazan jihar sun yi ibada cikin sauki.

Dangane da ciyarwar kuwa, Labbo ya bayyana cewa, hukumar ta kulla yarjejeniya da wani kamfani don ciyar da Alhazan jihar jigawa a kasar Saudiyya.

Ya ce, hukumar na da kwarin gwiwar cewa kamfanin zai cimma yarjejeniyar ciyar da abincin yadda ya dace.

Shugaban ya yi nuni da cewa,  mahajjatan da ke fama da rashin lafiya, wadanda ba za su iya cin abincin da aka tanadarwa Alhazai ba, za a basu kulawa ta musamman  wajen samar musu da abincin da ya dace da lafiyarsu.

Ya yi nuni da cewa, hukumar alhazai ta kasa NAHCON ta kayyade sama da naira miliyan takwas da dubu dari hudu (N8,457,685,59) a matsayin kudin aikin hajjin na bana.

Don haka ya yi kira ga maniyyatan da su kammala biyan kudadensu nan da  ranar 30 ga watan Janairun, 2025.

Yayin da yake yaba wa ma’aikatan hukumar bisa jajircewa wajen gudanar da ayyukansu, ya umarce su da su kara zage dantse don ganin an samu nasarar aikin Hajjin na bana.

Labbo ya bayyana godiya ga gwamnatin jihar karkashin jagorancin gwamna Umar Namadi, da kuma hukumar alhazai ta kasa NAHCON bisa goyon bayan da suke baiwa hukumar jin dadin alhazai ta jihar Jigawa.#Hajj2025

Usman Muhammad Zaria

Labarai

Labarai20 hours ago

Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu

Daga Nasir Malali  Dakarun Sashe na biyu na Rundunar Haɗin Gwiwa ta Arewa maso Yamma, Operation FANSAN YAMMA, sun ceto...

Labarai22 hours ago

NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta

Daga Yusuf Zubairu, Kaduna Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Yamma ta bayyana dawo da tsaro a matsayin babban fifikonta a...

Labarai5 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi6 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai1 week ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai1 week ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai1 week ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai1 week ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai1 week ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai1 week ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Mafi Shahara