Ilimi
Gwamnatin Tarayya da ke Gusau za ta Kafa Cibiyar Nazari kan Tarihi da Al’adun Zamfara
Daga Aminu Dalhatu
Shugaban Jami’ar Tarayya da ke Gusau (FUGUS), Farfesa Tukur Adamu, ya sanar da shirin jami’ar na kafa Cibiyar Bincike da Adana Tarihi da Al’adun Jihar Zamfara.
Farfesa Adamu ya bayyana hakan ne yayin da ya jagoranci tawagar shugabannin jami’ar ziyarar girmamawa ga Sarkin Anka kuma Shugaban Majalisar Sarakunan Jihar Zamfara, Alhaji Attahiru Muhammad Ahmad.
Sanarwar da Babban Jami’in Hulɗa da Jama’a na jami’ar, Jamilu Ibrahim Gusau, ya fitar ta ce ziyarar na daga cikin jerin ganawa da masu ruwa da tsaki da Shugaban jami’ar ke yi domin shimfiɗa alkiblar tafiyar da sabuwar gwamnatinsa.

A cewar Farfesa Adamu, cibiyar da ake shirin kafawa za ta mayar da hankali ne kan karewa, tattarawa da bunƙasa tarihin arziki da al’adun gargajiya na Jihar Zamfara.
Ya jaddada cewa wannan shiri na nuna muhimmancin da ake bai wa masarautu da kuma bukatar kare ilimin gargajiya domin amfanin al’umma masu zuwa.

Shugaban jami’ar ya tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta yi aiki kafada da kafada da Majalisar Sarakunan Jihar Zamfara domin tabbatar da cewa al’ummar jihar sun amfana da damar ilimi da ci gaba a FUGUS.
Ya yi kira ga Majalisar Sarakunan da ta jagoranci ƙoƙarin ƙara yawan ɗalibai ‘yan asalin Zamfara da ke samun gurbin karatu a jami’ar, yana mai cewa faɗaɗa damar samun ilimi mai zurfi zai taimaka wajen hanzarta ci gaban jihar baki ɗaya.

A nasa jawabin, Sarkin Anka, Alhaji Attahiru Ahmad, ya yaba wa Shugaban jami’ar da tawagarsa kan ziyarar, inda ya bayyana ta a matsayin farkon sabunta haɗin gwiwa tsakanin jami’ar da masarautu.
Ya ce ƙarfafa haɗin kai zai taimaka matuƙa wajen magance ƙalubalen zamantakewa da na ci gaba a jihar.

Sarkin ya kuma bayyana cewa Majalisar Sarakunan Jihar za ta yi aiki tare da jami’ar wajen shirya taruka da bitoci ga sarakunan gargajiya, tare da habbaka gudummawar da masu sarauta ke takawa a faɗin Jihar Zamfara.
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai7 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai7 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai7 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Labarai7 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai7 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
