Labarai
Ana Zargin Mutum 140 Sun Bace Bayan Nutsewar Jirgin Ruwan Iran a Gaɓar Sri Lanka
Rundunar sojin ruwan Sri Lanka ta tabbatar da ceto mutum 32 bayan samun kiran gaggawa daga jirgin ruwan sojin Iran mai suna IRIS Dena da safiyar yau Laraba.
Mai magana da yawun rundunar, Budhika Sampath, ya ce ko da yake lamarin ya faru ne a wajen iyakar ruwan ƙasarsu, amma yana cikin yankin da suke da alhakin aikin ceto, don haka wajibi ne su amsa kiran bisa ƙa’idojin ƙasa da ƙasa.
Ya ce sun tarar da wasu mutane na shawagi a kan ruwa, inda suka ceto su, sannan daga bisani bincike ya nuna cewa mutanen na cikin jirgin ruwan Iran din ne.
A cewarsa, takardun jirgin sun nuna cewa kimanin mutum 180 ne ke cikinsa, sai dai har yanzu ba a tabbatar da ainihin adadin waɗanda suka ɓace ba.
Tun da fari, sakataren ma’aikatar tsaron ƙasar, Air Vice Marshal Sampath Thuiyakontha, ya shaida wa BBC cewa ana kyautata zaton kusan mutum 140 sun ɓace.
Mai magana da yawun rundunar ya ƙara da cewa a lokacin da suka isa wurin domin aikin ceto, ba su hangi jirgin ba, amma sun ga tabon mai a saman ruwa da kuma kwale-kwalen ceton rai na shawagi.
Ya zuwa yanzu, rundunar sojin ƙasar ba ta iya tabbatar da abin da ya haddasa nutsewar jirgin ba.
BBC
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
