Labarai
Rundunar ‘Yansandan Kabi Ta Tabbatar da Mutuwar Mutane 33 Sakamakon Fashi da Makami
Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kebbi ta ƙara tsaurara matakan tsaro a Gundumar Bui da ke Ƙaramar Hukumar Arewa, bayan wani hari na satar shanu da ya auku a ranar Larabar da ta gabata.
Jami’in Hulɗa da Jama’a na rundunar, SP Bashir Usman, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da aka fitar ga manema labarai a Birnin Kebbi, babban birnin jihar.
Sanarwar ta ce an tura ƙarin jami’an tsaro da kayan aiki na musamman zuwa yankin, yayin da ake ci gaba da sintiri domin tabbatar da zaman lafiya. Rundunar ta nuna alhini matuƙa kan mutuwar mutane 33 marasa laifi, tare da miƙa ta’aziyya ga iyalan mamatan da daukacin al’ummar Arewa.
Binciken farko ya nuna cewa wasu ‘yan bindiga da ake kira Lakurawa ne suka shiga yankin domin satar shanu, kuma ana zargin sun tsallaka ne daga Ƙaramar Hukumar Gudu ta Jihar Sokoto.
Mutanen da abin ya shafa sun fito ne daga garuruwan Mamunu, Awasaka, Tungan Tsoho, Makangara, Kanzo, Gorun Naidal da Dan Mai Ago, inda suka yi yunƙurin mayar da martani, wanda a yayin haka ne aka yi mummunar arangama da ta yi sanadin asarar rayuka.
Rundunar ta jaddada cewa duk wani lamari da ya shafi ‘yan ta’adda masu makami na buƙatar haɗin kai da hukumomin tsaro. Don haka ta buƙaci jama’a da su rika kai rahoton duk wani motsi mai tayar da hankali ta hanyoyin tsaro da aka tanada, maimakon su ɗauki mataki da kansu, domin irin waɗannan arangama na da matuƙar haɗari.
Ta kuma bayyana cewa ana ci gaba da gudanar da ayyukan musamman domin kamo waɗanda suka aikata laifin, hana sake aukuwar irin haka, da kuma ƙarfafa hanyoyin samar da bayanan gaggawa.
Rundunar ta bayar da lambobin wayar ɗakin kula da bayanai kamar haka: 08038797644 da 09015888578 domin kai rahoto cikin gaggawa.
REL SANI DUTSINMA
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
