Labarai
Karamar Hukumar Birnin Kudu ta Raba Kayan Tallafin Ramadan ga Marasa Galihu
Daga Usman Muhammad Zaria
Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kudu a Jihar Jigawa ya raba kayan tallafin Ramadan ga marasa galihu a yankin.
Mai ba Shugaban shawara na musamman kan dabarun aiki, Malam Badamasi Muhammad Musa, wanda ya jagoranci rabon, ya bayyana cewa kayayyakin tallafin sun hada da shinkafa da gero da sauransu.
A cewarsa, jerin rabon kayan abincin na da nufin tallafawa marasa galihu a lokacin watan mai alfarma na Ramadan.
Ya ce wannan karamci wata alama ce ta kudurin Dakta Builder Muhammad Uba na taimakawa mabukata da kuma inganta jin dadin al’umma a karamar hukumar.

Ya kara da cewa shugaban karamar hukumar ya dade yana jaddada muhimmancin hidimar al’umma da kyautata zamantakewa, musamman a lokacin Ramadan.
Don haka, Malam Badamasi Muhammad Musa ya yi kira ga masu hannu da shuni da su yi koyi da Dakta Muhammad Uba, tare da ba da gudunmawa wajen tallafa wa mabukata a wannan lokaci.
Ya kuma bayyana fatan cewa wannan tallafi zai taimaka matuka wajen karfafa hadin kai da zaman lafiya a karamar hukumar Birnin Kudu da ma jihar baki daya.
Rediyon Najeriya ta ruwaito cewa ana sa ran ci gaba da rabon kayan a kwanaki masu zuwa, inda za a mayar da hankali kan masu rauni a cikin al’umma, ciki har da tsofaffi, zawarawa da marayu.
-
Labarai4 days agoHukumar Alhazai Ta Jigawa Ta Bayyana Alhininta Bisa Rasuwar Suleiman Usman
-
Fasaha3 days agoNASENI Ta Ƙarfafa Horar da Sana’o’i da Fasahar Jiragen Sama Marasa Matuki a Kaduna
-
Labarai3 days agoNSCDC Ta Kama Wanda Ake Zargi Da Safarar Mutane A Zamfara
-
Labarai2 days agoGwamna Uba Sani Ya Ce Bunƙasa Ƙwarewa Na Da Muhimmanci Ga Farfaɗo Da Tattalin Arziki
-
Labarai2 days agoGwamnatin Tarayya Ta Ɗauki Matakan Gaggawa Bayan Tabbatar da Ebola a Birnin Tarayya
-
Labarai2 days agoGwamnatin Zamfara Ta Nuna Damuwa Kan Ƙaruwar Hare-Haren ’Yan Bindiga
-
Labarai2 days ago’Yan Sanda Sun Kama Wanda Ake Zargi da Fashi da Makami A Kano
-
Labarai2 days agoTajudeen Zai Bayyana Rahoton Ayyukan Tinubu Cikin Kwanaki 14
