Connect with us

Labarai

Tawagar Gidan Rediyon Tarayya Kaduna ta Kai Ziyarar Aiki Fadar Gwamnatin Jigawa

Published

on

Daga Usman Muhammad Zaria

Mai rukon mukamin shugaban gidan Rediyon Tarayya na Kaduna, Malam Lawal Ali Garba, ya sake jaddada kudurin gidan rediyon na kara karfafa hadin gwiwa da Gwamnatin Jihar Jigawa.

Malam Lawal Ali Garba, wanda ya jagoranci tawagar shugabannin gidan rediyon zuwa Fadar Gwamnatin yayin ziyarar girmamawa ga gwamnan, ya ce sun kai ziyarar ce da nufin kara dankon hulda da masu ruwa da tsaki tare da kara inganta kyakkyawar alakar da ke tsakanin Rediyon da gwamnatin jihar ta Jigawa.

Ya isar da godiyar Babban Daraktan Rukunin gidajen Rediyon Tarayya , Dakta Mohammad Bulama, bisa abin da ya bayyana a matsayin ci gaba da goyon bayan da Gwamnatin Jigawa ke bai wa gidan rediyon.

Ya kuma yabawa Gwamna Namadi kan nasarorin da gwamnatinsa ta samu a bangarori daban-daban na ci gaba.

Mai rukon mukamin gidan rediyon ya bayyana nasarorin da aka samu a fannin ilimi, ciki har da gyaran makarantu sama da 100, zuba jari na biliyoyin naira a tallafin karatu karkashin shirin Danmodi Students Care, da kuma daukar kwararrun malamai don karfafa ingancin koyarwa a matakin ilimin bai daya.

Haka kuma ya yaba da ci gaban da aka samu a bangaren lafiya, inda ya ambaci daukar ma’aikatan lafiya da kuma farfado da tsarin bada magani kyauta ga yara da mata masu juna biyu a matsayin abin a yaba.

A cewarsa, aiwatar da mafi karancin albashi na Naira 70,000 da kuma shirye-shiryen tallafawa ma’aikata na kara nuna kudurin gwamnatin wajen inganta walwalar jama’a.

Lawal Ali Garba ya kuma yabawa gwamnatin jihar kan zuba jari a bangarorin noma, ababen more rayuwa, gidaje, bunkasa fasahar sadarwa, yaki da cin hanci da rashawa, da shirye-shiryen jin kai, musamman shirin ciyar da marasa galihu a watan Ramadan.

Ya tabbatar wa gwamnan cewa gidan Rediyon Najeriya Kaduna zai ci gaba da bayar da sahihan  rahotanni bisa kwarewa da adalci kan ayyukan gwamnati, musamman yayin da ake tunkarar zaben shekarar 2027, tare da ci gaba da sauke nauyinsa na wayar da kan jama’a da ilmantar da su.

Ziyarar ta hada da gabatar da wata takardar yabo ga Gwamna Namadi domin karrama shi bisa hidimarsa ga al’ummar Jihar Jigawa da kokarinsa na inganta zaman lafiya, ci gaba da kuma kusantar gwamnati da jama’a.

Da yake mayar da martani, Gwamna Umar Namadi ya nuna godiyarsa kan ziyarar tare da bayyana Rediyon Najeriya Kaduna a matsayin kafar yada labarai mai daraja wadda ta dade tana aiki da kwarewa da jajircewa

Ya gode wa tawagar shugabannin gidan rediyon kan haska nasarorin da gwamnatinsa ta samu, yana mai cewa yawan masu sauraron tashar ya taimaka wajen isar da manufofi da shirye-shiryen gwamnati ga jama’a.

Gwamnan ya jaddada muhimmancin ci gaba da karfafa hadin gwiwar, yana mai bayyana rediyo a matsayin daya daga cikin hanyoyin da suka fi tasiri wajen isa ga al’ummomin karkara.

Ya kuma lura cewa duk da karuwar amfani da kafafen sada zumunta, Rediyo na ci gaba da kasancewa kafar sadarwa mai karfi da amincewa a wajen jama’a.

Gwamna Namadi ya sake tabbatar da kudurin gwamnatinsa na ci gaba da aiki kafada da kafada da Rediyo Najeriya Kaduna domin tabbatar da cewa ana isar da shirye-shiryen gwamnati yadda ya kamata don amfanin al’ummar Jihar Jigawa.

Labarai

Labarai4 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi5 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai6 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai6 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai6 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai6 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai6 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai6 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Ilimi7 days ago

Zamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta

Daga Aminu Dalhatu  Hukumar Ilimin Bai-daya ta Jihar Zamfara, ZSUBEB, ta kaddamar da shirin shigar da yara makaranta na shekarar...

Labarai7 days ago

Gwamnan Kebbi Ya Yabi WAMY Kan Jinya Kyauta Ga Marasa Lafiya

Daga Sani Dutsinma Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya yaba wa Ƙungiyar Matasa Musulmi ta Duniya (WAMY) kan shirya aikin...

Mafi Shahara