Connect with us

Labarai

Masu Tasiri a Kafafen Sada Zumunta sun samu horo kan RMNCAH+N, Tsarin Iyali da Rigakafin Cin Zarafin Mata

Published

on

Ƙungiyar Centre for Communication and Social Impact (CCSI) tare da haɗin gwiwar abokan aikin ta na EngenderHealth Consortium sun shirya taron horo na yini ɗaya a Kano domin ƙarfafa ƙwarewar ’yan jarida da masu tasiri a kafafen sada zumunta (social media influencers) wajen yada sahihan bayanai da tallafawa manufofin kiwon lafiya da daidaito tsakanin jinsi.

 

Taron, mai taken “Daga Masu Bi zuwa Masu Faɗa Aji: Amfani da Kafafen Sada Zumunta wajen Yaɗa Sawun Lafiya da Daidaito”, ya mayar da hankali ne kan batutuwan Reproductive, Maternal, Newborn, Child, and Adolescent Health plus Nutrition (RMNCAH+N), Family Planning (FP), da Gender, Youth, and Social Inclusion (GYSI).

 

Manufar wannan horo ita ce canza masu tasiri a kafafen sada zumunta zuwa ƙwararrun masu fafutukar yaɗa ilimin lafiya da canjin halayyar jama’a ta hanyar amfani da hujjoji, ladabi, da al’adun da suka dace da al’umma.

 

A jawabinsa na budewa, Atiku Muhammad Auwal, Manajan Ayyukan Wayar da Kai na CCSI, ya bayyana cewa manufar taron ita ce samar wa masu tasiri a kafafen sada zumunta da ilimi da dabaru domin su zama masu faɗakarwa kan batutuwan RMNCAH+N, Tsarin Iyali, da Daidaito tsakanin jinsi.

 

Ya ce, horon zai taimaka musu wajen jan hankalin gwamnati da al’umma kan muhimman batutuwan lafiyar jama’a ta hanyar ingantacciyar fafutuka.

 

“Ta hanyar koyarwa daga masana da atisayen aiki, mahalarta sun koyi dabarun ƙirƙirar abun ciki na dijital mai tasiri, gaskiya, da tausayi ga waɗanda abin ya shafa, tare da hanyoyin yaki da labaran ƙarya da ƙarfafa tattaunawa mai haɗin kai,” in ji shi.

 

A cikin gabatarwarta mai taken “Matsayin RMNCAH+N, FP da GBV a Jihar Kano da rawar da masu tasiri ke takawa wajen kawo sauyi”, Dr. Mansurah, mai kula da shirye-shiryen Maternal, Newborn and Child Health (MNCH) a jihar, ta bayyana manyan ƙalubale da ke fuskantar sashen lafiya a Kano.

 

Ta ambaci matsalolin kamar rashin daidaiton rarraba cibiyoyin lafiya (PHCs), ƙarancin ƙwararrun ma’aikatan haihuwa, gibin kayan aiki da gini, ƙarancin kayan lafiya, ƙarancin kwarin gwiwar ma’aikata, raunin tsarin bayanai, da kuma rashin haɗin kan al’umma.

 

Shi kuwa Mataimakin Shugaban Ƙungiyar Ƴan Jarida ta Najeriya (NUJ) reshen Kano, Kwamared Mustapha Gambo Muhammad, ya jaddada cewa NUJ na gaba-gaba wajen yaƙi da cin zarafin mata da inganta ilimin lafiya, tsare iyali, da daidaito tsakanin jinsi.

 

Ya tabbatar da kudirin ƙungiyar wajen ci gaba da wayar da kai ta hanyar kafafen sada zumunta da rahotanni masu inganci.

 

A nata jawabin, Khadijah Abdullahi Yahaya daga Arewa Radio, ta jaddada rawar da masu tasiri da kafafen watsa labarai ke takawa wajen tallafawa shirye-shiryen tsare iyali da RMNCAH+N.

 

Ta yi kira da a ƙara haɗin kai da bayar da dama ga jama’a su rika bayyana irin ƙalubalen da suke fuskanta a cikin al’ummarsu.

 

Taron ya ƙunshi gabatarwa masu mu’amala, tambayoyi da amsoshi tare da masana lafiya, da damar haɗa kai tsakanin masu tasiri, ’yan jarida, da masu ruwa da tsaki a harkokin lafiya.

 

Khadijah Aliyu

Labarai

Labarai3 days ago

Ƙungiyar Ci gaban Al’ummar Saminaka Ta Bai Wa ‘Yan Sanda Injin Hilux Don Ƙarfafa Tsaro

Ƙungiyar Ci gaban Al’ummar Saminaka SAPPEF a ƙaramar hukumar Lere ta Jihar Kaduna ta bayar da gudummawar sabon injin motar...

Labarai5 days ago

Gwamnatin Nasarawa ta Nada Sabon Osu Ajiri na Masarautar Udege

Daga Aliyu Muraki  Gwamnatin Jihar Nasarawa ta amince da nadin Suleiman Ahmed Eko a matsayin sabon Osu Ajiri na masarautar...

Ilimi6 days ago

Gwamnatin Zamfara Za Ta Gina Dakunan Kwanan Dalibai a Jami’ar Talata Mafara

Daga Aminu Dalhatu Gwamnatin Jihar Zamfara ta sanar da shirin gina dakunan kwanan dalibai da kuma samar da motocin sufuri...

Ilimi6 days ago

Gwamnatin Tarayya Ta Yi Alkawarin Inganta Hanyoyi, Ruwa da Wutar Lantarki a Jami’ar FUD

Daga Usman Muhammad Zaria Minista a Ma’aikatar Ayyuka, Barrista Bello Muhammad Goronyo, ya yi alkawarin shiga tsakani wajen samar da...

Labarai6 days ago

‘Yan Sanda Sun Cafke ‘Yan Bindiga Da Ceto Wasu Da Aka Sace A Zamfara

Rundunar ‘yan sanda ta jihar Zamfara ta ce ta samu nasarori a ƙoƙarinta na yaƙi da ta’addanci, inda ta ceto...

Labarai6 days ago

Tinubu: Sabbin Dokokin Haraji Za Su Kawo Wadata Yayinda Tsofaffi Suka Talauta ‘Yan Najeriya

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ce tsofaffin dokokin haraji na zamanin mulkin mallaka sun talauta ‘yan Najeriya, yana mai...

Labarai6 days ago

NSCDC Ta Gargadi Masu Laifi Da Barayin Kadarori A Kwara

Hukumar tsaro ta NSCDC a jihar Kwara ta gargadi masu aikata laifuka da masu lalata kadarorin gwamnati da su kauce...

Labarai6 days ago

Harin Shanga: Gwamnatin Tarayya Za Ta Tallafawa Iyalan Jama’an Tsaro da Aka Kashe

Daga Bello Wakili  Gwamnatin Tarayya ta tabbatar wa iyalan jami’an tsaro da aka kashe a wani harin baya-bayan nan da...

Labarai6 days ago

Kashim Shettima Ya Jagoranci Tawagar Gwamnatin Tarayya Zuwa Kebbi

Daga Sani Dutsinma Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya jagoranci wata babbar tawagar gwamnatin tarayya zuwa Jihar Kebbi domin yin...

Kasuwanci7 days ago

Majalisar Neja ta Amince da Dokar Hana Ayyukan Baban Bola a Unguwanni

Daga Aliyu Lawal  Majalisar Dokokin Jihar Neja ta amince da kudirin dokar daidaita ayyukan Baban bola da masu kasuwancin karafa...

Mafi Shahara