Labarai
Tinubu Ya Bayyana Alhininsa Bisa Harin Ta’addanci a Kauyen Ngoshe na Jihar Borno
Daga Bello Wakili
Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya bayyana alhinin sa tare da miƙa ta’aziyya ga iyalan waɗanda harin ta’addancin ya shafa a ƙauyen Ngoshe da ke Karamar Hukumar Gwoza ta Jihar Borno.
Shugaban ƙasar ya yi alhinin rasuwar mutane da ba su ji ba ba su gani ba, ciki har da jami’an soji, da kuma waɗanda suka rasu sakamakon harbin kuskure yayin da jiragen yaƙi ke kai hari ga ‘yan ta’addan da suka tsere.
Ya bayyana harin na ‘yan ta’addan a matsayin mummunan ta’adi da rashin tausayi ga al’umma marasa ƙarfi, tare da kira ga al’ummar Borno da sauran sassan ƙasar da kada su karaya.
Shugaba Tinubu ya kuma yaba wa sojojin bisa martanin gaggawa da suka mayar, wanda ya yi sanadiyyar kashe ‘yan ta’adda da dama tare da tilasta musu janyewa daga yankin.
Ya kuma umarci sojoji da sauran hukumomin tsaro da su gaggauta ceto mutanen da ‘yan ta’addan suka sace.
Bugu da ƙari, Shugaban ya umarci rundunar sojoji da ta ƙara ƙaimi wajen kare fararen hula a faɗin ƙasar da kuma hana kai hare-hare kan sansanonin soji musamman a yankin Arewa maso Gabas.
Shugaba Tinubu ya yi addu’ar Allah Ya ji ƙan waɗanda suka rasu a harin da kuma harbin kuskure, tare da miƙa ta’aziyya ga iyalansu da kuma Gwamnatin Jihar Borno.
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai1 day ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai1 day ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
