Labarai
Gwamnatin Kwara Ta Jaddada Kudurinta Na Kula Da Jin Daɗin Masu Harkar Sufuri
Gwamnatin Jihar Kwara ta bai wa masu harkar sufuri a jihar tabbacin ci gaba da kare muradunsu da jin daɗinsu.
Kwamishinan Sufuri na jihar, Lafia Korasabi, ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da Shugaban Ƙungiyar Masu Baburan Adaidaita Sahu ta Ƙasa (TOAN) a Ilorin.
Kwamishinan, wanda ya nuna rashin jin daɗinsa kan wasu halaye da ake samu, ya sake jaddada cewa bin ƙa’idojin tikitin da aka amince da su yana da muhimmanci wajen tabbatar da zaman lafiya, adalci da kuma kare muradun dukkan masu ruwa da tsaki.
Ya kuma bayyana cewa daga cikin jimillar kuɗin tikitin yau da kullum da ƙungiyar ke karɓa, Naira 200 kacal ne ke shiga asusun Gwamnatin Jiha ta hannun Hukumar Tara Haraji ta Jihar Kwara.
Saboda haka, ya nesanta gwamnatin daga zargin karɓar kuɗi fiye da ƙima daga masu harkar sufuri, yana mai cewa gwamnati na daraja gudunmawar da kowane mai sana’ar sufuri ke bayarwa ga tattalin arziƙi da zaman lafiyar al’umma a jihar.
Lafia Korasabi ya jaddada cewa gwamnatin na bai wa fifiko ga samar da yanayin aiki mai adalci da zai amfani masu sufuri da fasinjoji baki ɗaya.
Ya ƙara da cewa duk wani ƙin bin ƙa’ida ba wai kawai karya yarjejeniya ba ne, har ma barazana ce ga zaman lafiya da daidaiton ɓangaren sufuri a Jihar Kwara.
A nasa jawabin, Sakataren Dindindin na Ma’aikatar, Alhaji Salau Abdullahi, ya sake tabbatar da aniyar ma’aikatar na tabbatar da adalci, gaskiya da ci gaba da haɗin gwiwa da ƙungiyoyin sufuri.
Ya buƙaci shugabannin ƙungiyoyin da su ja kunnen mambobinsu tare da tabbatar da bin kuɗin harajin da aka amince da shi.
Alhaji Salau ya ce ci gaba da karɓar kuɗi fiye da ƙa’ida ya haifar da rashin jin daɗi a tsakanin masu sana’ar, wanda zai iya janyo rikice-rikicen da za a iya kauce wa matuƙar ba a ɗauki matakin gaggawa ba.
ALI MUHAMMAD RABIU
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
