Labarai
Gwamnatin Kebbi Za ta Raba Hatsi da Kayayyakin Aikin Gona ga Marasa Galihu
Daga Sani Dutsinma
Gwamnatin Jihar Kebbi ta kammala shirye-shiryen raba kayayyakin aikin noma da nau’o’in hatsi daban-daban ga mutane miliyan daya a fadin jihar.
Kayayyakin da za a raba sun hada da Shinkafa, Masara, Gero, Dawa, Famfunan ban-ruwa, injinan noma (power tillers), kayayyakin feshi da sauran su, domin inganta yawan amfanin gona, karfafa dorewar aikin noma da kuma rage radadin talauci.

Jihar Kebbi na da manoma kanana wadanda suka kai kusan kashi 95 cikin dari na yawan manoman jihar, kuma su ne ginshikin samar da abinci a jihar da ma kasa baki daya.
A cewarsa, ci gaba da tallafawa manoma da kayayyakin aiki na zamani zai kara musu kwarin gwiwa tare da taimakawa wajen samun girbi mai yawa, ta yadda jama’a za su samu wadataccen abinci har ma a samu damar fitar da shi zuwa kasashen waje.

Kwamishinan Aikin Noma na jihar, Alhaji Shehu Mu’azu, ya bayyana cewa kungiyoyin manoma da suka hada da na mata, da matasa da kuma masu bukata ta musamman za su amfana da shirin.
Ya kara da cewa, an tsara wannan shiri ne domin karfafa hada kan kowa a harkar noma, samar da damar yin noma a duk shekara da kuma tabbatar da wadatar abinci.
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai20 hours ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai22 hours ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
