Labarai
Hukuncin Kwamitin PAC kan Kudin NNPCL
Kwamitin Majalisar Dattawa kan Asusun Jama’a ya kira tsofaffin shugabannin NNPCL da shugabannin yanzu domin su bayyana dalla-dalla kan hanyoyin amfani da naira tiriliyan 210 a kamfanin.
Shugaban kwamitin, Sanata Ahmad Aliyu Wadada, ya bayar da wannan umarni ne bisa ikon da Kundin Tsarin Mulki da dokokin majalisa suka ba shi na kiran kowanne shugaban hukumar gwamnati domin bayyana duk wata mu’amalar kudi.
Sanata Wadada ya ce binciken majalisa ya samo asali ne daga abubuwan da kwamitin ya lura da su a cikin sarrafa kudade yayin duba rahoton babban mai binciken kudi na tarayya na shekarun 2019 da 2020.
Ya ce tun daga lokacin, kwamitin yana binciken bayanan kudade na NNPCL daga shekarar 2017 zuwa 2023, kuma binciken bai tsaya ba saboda an watsar da shi, sai dai saboda suna son yin cikakken bincike domin kada sakamakon ya kasance ba a fahimta ba.
Shugaban kwamitin ya kara da cewa, domin gudanar da wannan aiki yadda ya kamata, kwamitin ya nemi bayanan da suka dace daga NNPCL, kuma kamfanin ya bayar da su.
Kwamitin ya duba bayanan kudade da aka bincika na NNPCL daga 2017 zuwa 2023, wanda masu bincike na waje suka shirya, amma kwamitin bai gamsu gaba daya ba.
Kwamitin ya tabbatar da cewa zai ci gaba da huldar da duk masu ruwa da tsaki wajen gudanar da ayyukansa na majalisa da kuma tsaftace sashen mai da masana’antar man fetur domin ci gaban tattalin arzikin Najeriya.
Cov/ Bashir M
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
