Connect with us

Labarai

Hukumar Alhazai ta Jigawa ta Jinjinawa Hukumomin Tsaro Bisa Goyon Bayan da Suke Ba Ta

Published

on

Daga Usman Muhammad Zaria

Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Jigawa ta yi kira ga Hukumar Shige da Fice ta kasa da ta tabbatar da gudanar da ayyuka cikin sauƙi da tsari ga maniyyatan Hajjin shekarar 2026 yayin tantance su a Filin Jirgin Sama na Nuhu Muhammadu Sunusi.

Babban Daraktan hukumar, Alhaji Ahmed Umar Labbo ne ya yi wannan kiran yayin wata ganawa da Kwanturolan Hukumar Shige da Fice ta jihar a hedikwatar hukumar da ke Dutse, babban birnin jihar.

Ya bayyana cewa an shirya taron ne domin tattauna tsare-tsare da dabarun da za su inganta matakan tsaro domin tunkarar ayyukan Hajjin shekarar 2026.

A cewarsa, samar da ingantattun na’urorin tantancewa da tsare-tsare masu sauƙi zai taimaka matuƙa wajen rage wahalar da maniyyata ke fuskanta tare da tabbatar da jigilarsu a kan lokaci domin gudanar da aikin Hajjin shekarar 2026.

Alhaji Ahmed Umar Labbo ya kuma yi kira ga hukumomin tsaro da sauran masu ruwa da tsaki da su ba da cikakken haɗin kai domin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin maniyyata tun daga sansanin Alhazai har zuwa filin jirgin sama kafin tafiyarsu zuwa ƙasar Saudiyya.

Babban Daraktan ya gode wa dukkan hukumomin tsaro bisa ci gaba da goyon baya da haɗin kai domin cimma manufofin da ake buƙata.

A nasu jawabin, hukumomin tsaron sun tabbatar wa hukumar da cikakken goyon baya ga gwamnatin jihar.

Sun kuma yi alƙawarin taimakawa wajen samar da tsaro tare da tabbatar da jin daɗi da walwalar maniyyatan Hajji yayin gudanar da ayyukansu.

Labarai

Labarai4 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi5 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai6 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai6 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai6 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai6 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai6 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai6 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Ilimi7 days ago

Zamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta

Daga Aminu Dalhatu  Hukumar Ilimin Bai-daya ta Jihar Zamfara, ZSUBEB, ta kaddamar da shirin shigar da yara makaranta na shekarar...

Labarai7 days ago

Gwamnan Kebbi Ya Yabi WAMY Kan Jinya Kyauta Ga Marasa Lafiya

Daga Sani Dutsinma Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya yaba wa Ƙungiyar Matasa Musulmi ta Duniya (WAMY) kan shirya aikin...

Mafi Shahara