Labarai
Bankin Raya Kasashen Afirka Zai Samar da Shirin Bunƙasa Aikin Noma a Jigawa
Daga Usman Muhammad Zaria
Gwamnatin Jihar Jigawa ta bada tabbacin baiwa bankin raya kasashen Afrika cikakken goyan bayan ta domin cika sharudda da ka’idojin da ake bukata domin amfanin al’ummar jihar.
Mataimakin Gwamnan jihar Injiniya Aminu Usman Gumel ya bada wannan tabbacin a lokacin da tawagar bankin ta ziyarci ofishin sa dake Dutse.

Yace Gwamnatin jihar ta himmatu wajen cika ka’idojin saboda muhimmancin su ga al’umma, musamman yadda jihar ta bi sahun wasu jihohi biyar da suke cikin shirin.
Tun farko a nasa jawabin, jagoran tawagar Bankin,ta bakin Babangida Shehu yace sun ziyarci ofishin mataimakin Gwamnan ne domin tattauna batutuwan da suka shafi cika sharuddan bankin, domin jihar ta samu nasarar amfana da tsare tsaren bankin a bangarorin bunkasa aikin gona da gina kamfanoni domin bunkasa tattalin arziki.
Ya kara da cewar tawagar bankin ta gamsu da tsare tsaren jihar Jigawa wajen cika ka’idojin a tsakanin sauran takwarorin ta jihohi biyar da suke cikin shirin.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
