Labarai
Masarautar Hadejia ta Raba Zakkar Kayan Amfanin Gona da Dabbobi a Garin Unik
Daga Usman Muhammad Zaria
Kwamitin zakka na masarautar Hadejia ya raba zakkar kayayyakin amfani gona da dabbobi da kudin su ya tasamma Naira Miliyan 71 a garin Unik dake gundumar Auyo a Jihar Jigawa.
A jawabin sa, Sakataren kwamitin Malam Isma’ila Garba Barde ya ce kwamitin ya raba zakkar bahunan shinkafa 1,046 da buhunan dawa 192 dari da shanu guda 4 da kuma tumaki 13 ga mabukata.

A jawabin sa, Baban Limamin Masarautar Hadejia Sheikh Yusuf Abdulrahaman ya bayyana Zakka a matsayin daya daga cikin shika-shikan addinin musulunci da ta wajaba akan masu hali.
Shugaban karamar hukumar Auyo, Alhaji Biliyaminu Ahmed Adamu Kafur ya godewa kwamitin bisa jajircewa da Kuma bada lokacin su don ganin ana fidda hakkin Allah.
Ya tabbatar da cewar karamar hukumar zata ci gaba da bada duk wani goyan baya da ake bukata.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
