Labarai
NCAA ta Yaba wa Hukumar Alhazai ta Jihar Kebbi Bisa Kyakkyawan Tanadin Aikin Hajji
Daga Sani Dutsinma
Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta Najeriya (NCAA), ta yaba da kokarin Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kebbi bayan duba kayayyakin aiki da shirye-shiryen da aka tanada domin gudanar da aikin Hajji cikin nasara.
Shugaban tawagar binciken, Injiniya Abba Shu’aibu Babagana ne ya bayyana hakan yayin ziyarar aiki da ya jagoranta zuwa jihar ta Kebbi.
A yayin ziyarar, jami’an NCAA sun duba muhimman wurare da dama a sansanin Alhazai na Kauran Gwandu Hajj Camp domin tantance yadda aka shirya kafin fara jigilar maniyyata zuwa aikin Hajjin bana.
Sun kuma ziyarci Cibiyar ICT, inda ake gudanar da rajista da sarrafa bayanan maniyyata ta hanyar fasahar zamani.
Hakazalika, tawagar ta duba Dakin Taro da ake amfani da shi wajen gudanar da tarurruka, da kuma Dakin Tantancewa inda ake gwajin lafiya, tabbatar da takardu, da sauran matakan tantancewa domin tabbatar da ganin dukkan maniyyata sun cika ka’idojin tafiya kafin a tafi aikin Hajji.
Jami’an NCAA sun kuma zagaya harabar sansanin Alhazan gaba ɗaya, inda suka nuna gamsuwa da tsafta, tsari, da kuma kayayyakin da aka tanada domin tallafawa maniyyata yayin shirye-shiryen tafiya.
A cewar jami’an, kayayyakin more rayuwa da tsare-tsaren da Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kebbi ta samar, na nuna irin ƙoƙarin gwamnatin jihar wajen tabbatar da cewa an gudanar da aikin Hajji cikin tsari, aminci, da inganci.
Ziyarar na daga cikin binciken da hukumar ke yi akai-akai domin tabbatar da cewa jihohi suna bin ƙa’idojin sufurin jiragen sama da ka’idojin aiki da ake buƙata domin nasarar jigilar maniyyata zuwa Saudi Arabia.
-
Labarai6 days agoAna Zargin Mutum 140 Sun Bace Bayan Nutsewar Jirgin Ruwan Iran a Gaɓar Sri Lanka
-
Labarai7 days agoJam’iyyar APC Ta Zaɓi Sabbin Shugabanni a Jihar Kano
-
Labarai5 days agoRamadan: Sarkin Kauru Ya Bukaci a Kara Karfafa Tsaro Tare da Tallafawa Marasa Galihu
-
Labarai7 days agoGwamnatin Jigawa Za Ta Kashe Miliyoyin Naira Don Sayen Gidaje 96 Daga Gwamnatin Tarayya
-
Labarai4 days agoKaramar Hukumar Birnin Kudu ta Nemi Hadin Kan Kungiyar ‘Yan Achaba Wajen Dakile Matsalar Tsaro
-
Labarai4 days agoSojojin Najeriya Sun Karɓi Motocin Yakin Da Aka Kera A Cikin Ƙasa
-
Ilimi6 days agoGwamnatin Tarayya da ke Gusau za ta Kafa Cibiyar Nazari kan Tarihi da Al’adun Zamfara
-
Labarai4 days agoMajalisar Dokokin Jihar Kano Ta Fara Shari’ar Tsige Mataimakin Gwamna Aminu Abdulsalam
