Labarai
Karamar Hukumar Birnin Kudu ta Nemi Hadin Kan Kungiyar ‘Yan Achaba Wajen Dakile Matsalar Tsaro
Daga Usman Muhammad Zaria
Shugaban Karamar hukumar Birnin Kudu dake Jihar Jigawa, Dr. Builder Muhammad Uba ya kaddamar da sabbin shugabannin rikon kwarya na kungiyar ‘yan Achaba na yankin.
A Jawabin da ya gabatar a yayin kaddamarwar a fadar Hakimi, Dr Muhammad Uba yace an nada sabbin shugabanin ne domin samun zaman lafiya a tsakanin su.

Ya kuma hore su da su bi dokoki da ka’idojin kungiya, tare da baiwa Karamar hukumar hadin kai da goyan baya wajen kai rahotan zuwan bakin ‘yan achaba dan tabbatar da tsaro.
Builder Muhammed Uba ya ba su tabbacin samun hadin kai da goyan bayan Karamar hukumar, ya kuma nuna rashin jin dadi da yawan sace sacen babura a yankin.

Kazakika, ya yabawa Gwamna Umar Namadi bisa kokarin sa na tabbatar da tsaro.
Shi ma a nasa jawabin, Hakimin Birnin Kudu Alhaji Hussaini Hassan jibrin ya bada shawarar yiwa Babura lambobi domin samun saukin ganewa tare da basu horo dan kwarewa akan aikin achaba.

A jawaban su daban daban, Shugaban ‘yan achaba na jihar, Abbas Abdulkadir da sakataren kungiyar, Yau Muhammad sun yabawa shugaban karamar hukumar bisa daukar matakin nada shugabannin riko na kungiyar ‘yan achaba na yankin.
A jawabin sa na godiya, sabon shugaban rikon kungiyar ‘yan Achaba na yankin Auwalu Ibrahim ya bada tabbacin yin aiki bil hakki da gaskiya.
-
Labarai6 days agoIran ta Tabbatar da Kisan Ayatollah Khamenei a Hare-haren Amurka da Isra’ila
-
Labarai4 days agoHukumar Kula da Kogin Benuwe ta Dauki Matakin Yashe Laka da Yashi da ke Barazana ga Noman Rani
-
Labarai4 days agoGwamna Namadi Ya Raba Tallafin Ramadan ga Ma’aikata da Marasa Galihu
-
Labarai7 days agoBankin Raya Kasashen Afirka Zai Samar da Shirin Bunƙasa Aikin Noma a Jigawa
-
Labarai7 days agoMasarautar Hadejia ta Raba Zakkar Kayan Amfanin Gona da Dabbobi a Garin Unik
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa ta Gargadi ‘Yan Kwangila Kan Ingancin Abincin Ramadan
-
Labarai5 days agoGwamnatin Kwara Ta Jaddada Kudurinta Na Kula Da Jin Daɗin Masu Harkar Sufuri
-
Labarai3 days agoAna Zargin Mutum 140 Sun Bace Bayan Nutsewar Jirgin Ruwan Iran a Gaɓar Sri Lanka
