Connect with us

Ilimi

Hukumomin Ilimi a Jihar Jigawa Sun Kare Kasafin Kudinsu a Gaban Majalisa

Published

on

Daga Usman Muhammad Zaria 

Hukumar bunkasa ilimin manya ta jihar Jigawa tace za ta kashe naira milyan 400 wajen gudanar da harkokin ta a sabuwar shekara ta 2026.

Shugaban hukumar. Dr. Abbas Abubakar Abbas, ya bayyana haka lokacin kare kiyasin kasafin kudin hukumar a gaban kwamatin ilimi matakin farko na majalisar dokokin jihar Jigawa.

Dr Abbas Abubakar Abbas ya ce hukumar za ta yi amfani da kudaden wajen inganta shirye shiryen koyon karatu da rubutu ga manya maza da mata da na ci gaba da karatu don kammala karatun sakandare da na masu son sake jarrabawar sakandire da koyon karatu ta Rediyo da cibiyoyi daban daban da ke fadin jihar.

Shi ma da ya ke kare kiyasin kasafin kudin hukumarsa , shugaban hukumar makarantun Tsangaya, Dr. Hamisu Maje, ya ce sun yi kiyasin naira milyan dubu 3 da milyan 500 tare da kudurin kammala aikin ginin makarantun Tsangaya guda 3 da ke Ringim da Kafin Hausa da Dutse.

Ya ce an yi tanadi domin kafa cibiyar koyar da sana’oi da gidajen alarammomi da masallaci tare da samar da ruwan sha da wutar lantarki a kowacce makaranta.

Dr. Hamisu Maje ya kuma bayyana cewar hukumar za ta gyara makarantun Tsangaya guda 7 da aka gada daga gwamnatin tarayya da ke sashen jihar domin karfafa tsarin ilimin makarantun Tsangaya na zamani.

A daya bangaren kuma, kwalejin fasaha ta jihar da ke Dutse da Kuma hukumar bada tallafin karatu ta jihar sun kare kiyasin kasafin kudadensu a gaban kwamatin kula da manyan makarantu na majalisar dokokin jihar Jigawa.

Da ya ke kare kiyasin kasafin kudin, shugaban kwalejin fasaha ta jihar da ke Dutse, Dr. Ahmad Badayi, ya ce sun yi kiyasin fiye da naira milyan 700 wadda daga ciki an kebe naira milyan 330 domin sayo kayayyakin aiki a dakin gwaje-gwaje da koyon aikin hannu da gyaran ofisoshi, yayin da za a yi amfani da ragowar kudaden wajen kammala manyan ayyuka.

Shi ma da ya ke kare kiyasin kasafin kudin hukumar sa, shugaban hukumar bada tallafin karatu ta jihar Malam Sa’idu Magaji, ya ce sun yi kiyasin kashe naira milyan dubu 10 domin bada tallafin karatu na cikin gida da na kasashen waje.

A nasa jawabin, shugaban kwamatin kula da ilimin manyan makarantu na majalisar dokokin jihar Jigawa kuma wakilin mazabar Sule Tankarkar Alhaji Muhammad Abubakar Sa’id, ya jaddada bukatar ganin masu ruwa da tsaki a bangaren manyan makarantu sun yi dukkan mai yiwuwa domin inganta harkokin ilimi mai zurfi a sabuwar shekara.

 

 

Labarai

Labarai1 hour ago

Ramadan: Tinubu Ya Kara Jaddada Kudirinsa na Inganta Rayuwar Jami’an Soji

Daga Bello Wakili  Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana godiya ga jami’an Rundunar Sojin Najeriya bisa sadaukarwar da suke...

Labarai2 hours ago

Tinubu Ya Bayyana Alhininsa Bisa Harin Ta’addanci a Kauyen Ngoshe na Jihar Borno

Daga Bello Wakili  Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya bayyana alhinin sa tare da miƙa ta’aziyya ga iyalan waɗanda harin ta’addancin...

Labarai8 hours ago

Karamar Hukumar Birnin Kudu ta Nemi Hadin Kan Kungiyar ‘Yan Achaba Wajen Dakile Matsalar Tsaro

Daga Usman Muhammad Zaria Shugaban Karamar hukumar Birnin Kudu dake Jihar Jigawa, Dr. Builder Muhammad Uba ya kaddamar da sabbin...

Labarai8 hours ago

Tsarin Kundin Shirin Bunkasa Samarda Abinci Mai Gina Jiki

Majalisar Kasa Kan Abinci da Gina Jiki, wacce Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shettima ke jagoranta, ta kafa wani kwamiti na...

Labarai8 hours ago

Hukuncin Kwamitin PAC kan Kudin NNPCL

Kwamitin Majalisar Dattawa kan Asusun Jama’a ya kira tsofaffin shugabannin NNPCL da shugabannin yanzu domin su bayyana dalla-dalla kan hanyoyin...

Labarai8 hours ago

Kotun Kwara Ta Yanke Wa Mutane Biyu Hukuncin Kisa Ta Rataya

Babban Kotun Jihar Kwara dake Ilorin, karkashin jagorancin Alƙali Ahmed Aliyu Gegele, ta yanke wa mutane biyu hukuncin kisa ta...

Labarai8 hours ago

Majalisar Dokokin Jihar Kano Ta Fara Shari’ar Tsige Mataimakin Gwamna Aminu Abdulsalam

Majalisar Dokokin Jihar Kano (KNHA) ta fara shari’ar tsige Mataimakin Gwamna Aminu Abdulsalam bayan tuhumar aikata manyan laifuka, amfani da...

Labarai8 hours ago

Uwargidan Gwamnan Jihar Kabi Ta Yaba Da Shirin Agajin Tukur Wasoso

Uwargidan Gwamnan Jihar Kebbi, Hajiya Zainab Nasare-Nasir, ta yi kira ga mutane masu arziki da su dauki darasi daga aikin...

Labarai8 hours ago

Sojojin Najeriya Sun Karɓi Motocin Yakin Da Aka Kera A Cikin Ƙasa

Sojojin Najeriya sun karɓi motocin Vanquisher Light Armoured Personnel Carriers da aka kera a cikin ƙasa daga kamfanin sarrafa makamai...

Labarai8 hours ago

FUGUS Za Ta Kafa Cibiyar Tarihi da Al’adu ta Zamfara

Shugaban Jami’ar Tarayya dake Gusau (FUGUS), Farfesa Tukur Adamu, ya bayyana shirin kafa Cibiyar Bincike da Rubuce-Rubuce kan Tarihi da...

Mafi Shahara