Labarai
Ma’aikatar Ayyuka da Sufuri ta Jigawa Ta Bada Kiyasin Kasafin Kudi na Sama da Naira Biliyan 161
Daga Usman Muhammad Zaria
Ma’aikatar Ayyuka da Sufuri ta Jihar Jigawa ta yi kiyasin kashe kudade miliyan dubu 161 da milyan 336 domin gudanar da ayyukan hanyoyin mota da harkokin yau da kullum a sabuwar shekara ta 2026.
Babban sakataren ma’aikatar, Malam Ahmad Isah, ya bayyana haka lokacin da ya ke kare kiyasin kasafin kudin ma’aikatar a gaban kwamatin ayyuka da sufuri na majalisar dokokin jihar Jigawa.
Babban Sakataren ya yi bayanin cewar, za a yi amfani da mafi yawan kudaden ne wajen gudanar da ayyukan hanyoyin mota tsakanin gariruwa da hanyoyin burji da kuma titunan cikin gari.
Yana mai cewar, haka kuma za a gudanar da ayyukan hanyoyi a manyan makarantun jihar ciki har Jami’ar Sule Lamido da ke Kafin Hausa da kwalejin fasaha da ke Dutse da cibiyar binciken aikin gona ta Kazaure, da kwalejin koyon aikin lafiya matakin farko da ke Jahun da sauransu.
Sai dai kuma babban sakataren ya koka dangane da bukatar daukar injiniyoyi domin aiki a ma’aikatar da hukumar gyaran hanyoyin mota JIRMA da kuma daukar sabbin jami’an duba lafiyar ababen hawa wato V.I.O, idan aka yi la’akari da karancin ma’aikata saboda masu yin ritaya.
Alhaji Ahmad Isah ya kara da cewar ma’aikatar tana kokarin cimma yarjajjeniya da makarantar koyon tukin jirgin sama ta kasa da ke Zaria domin amfani da filin jirgin sama na Dutse a matsayin sansanin koyon tukin jirgin sama.
Kazalika, ya ce makarantar koyon tukun mota da ke karamar hukumar Birnin Kudu za ta amfana da wasu ayyuka a sabuwar shekara.
A nasa jawabin, shugaban kwamatin ayyuka da sufuri na majalisar dokokin jihar Jigawa kuma wakilin mazabar Bulangu Alhaji Yusuf Ahmad Soja, ya yi addu’ar Allah Ya sa kasafin kudin ya karfafa cigaban jihar nan a sabuwar shekara.
-
Labarai6 days agoAna Zargin Mutum 140 Sun Bace Bayan Nutsewar Jirgin Ruwan Iran a Gaɓar Sri Lanka
-
Labarai6 days agoJam’iyyar APC Ta Zaɓi Sabbin Shugabanni a Jihar Kano
-
Labarai5 days agoRamadan: Sarkin Kauru Ya Bukaci a Kara Karfafa Tsaro Tare da Tallafawa Marasa Galihu
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Za Ta Kashe Miliyoyin Naira Don Sayen Gidaje 96 Daga Gwamnatin Tarayya
-
Labarai4 days agoKaramar Hukumar Birnin Kudu ta Nemi Hadin Kan Kungiyar ‘Yan Achaba Wajen Dakile Matsalar Tsaro
-
Labarai4 days agoSojojin Najeriya Sun Karɓi Motocin Yakin Da Aka Kera A Cikin Ƙasa
-
Labarai4 days agoMajalisar Dokokin Jihar Kano Ta Fara Shari’ar Tsige Mataimakin Gwamna Aminu Abdulsalam
-
Ilimi6 days agoGwamnatin Tarayya da ke Gusau za ta Kafa Cibiyar Nazari kan Tarihi da Al’adun Zamfara
