Connect with us

Labarai

Kaduna Ta Kaddamarda Shirin Rabon Maganin Kariya Daga Cutar Dundumi

Published

on

 

Daga Khadija Kubau

 

Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Kaduna tareda haɗin gwiwar kungiyar Sightsavers sun kaddamar da shirin raba magunguna domin kare al’umma daga kamuwa daga cutar dundumi River Blindness a jihar.

 

An gudanar da bikin kaddamar da shirin ne a Cibiyar Kula da Lafiya ta Matakin Farko (PHC) da ke Kinkinau a Karamar Hukumar Kaduna ta Kudu, inda jami’an lafiya da shugabannin al’umma da kuma abokan hulɗa suka halarta domin tallafawa yaki da cututtukan da aka yi watsi da su wato Neglected Tropical Diseases

 

Kwamishinar Lafiya ta Jihar, Hajiya Umma K. Ahmed, wadda ta kaddamar da shirin rabon magungunan, ta bayyana cewa za a gudanar da shirin ne a kananan hukumomi shida daga cikin kananan hukumomi 23 na jihar.

 

Kwamishinar, wadda Daraktan Kiwon Lafiyar Jama’a, Dakta Abubakar Sadiq Idris ya wakilta, ta ce an zabi Karamar Hukumar Kaduna ta Kudu ne domin fara shirin saboda bincike ya nuna cewa akwai mutane da dama da cutar ta fi shafa a yankin.

 

Ta kara da cewa za a raba magungunan ga mutane masu shekaru biyar zuwa sama domin dakile yaduwar cutar tare da rage illolinta a cikin al’umma.

 

Da take jawabi a wajen taron, Madam Gong, wadda ta wakilci Daraktar kungiyar Sightsavers Nigeria, Farfesa Joy Shuaibu, ta roki al’umma da su rika shan magungunan kamar yadda jami’an lafiya suka umarta.

 

Ta jaddada cewa hadin kan al’umma yana da matukar muhimmanci wajen cimma burin kawar da cutar.

 

Tun da farko, jami’ar kulada Cututtukan da aka yi watsi da su, (NTD), Zainab Haruna, ta bayyana manufofin shirin, inda ta ce an kirkiro shi ne domin rage yawaitar cutar ta hanyar raba magungunan kariya kyauta ga al’umma.

 

Ta kuma bukaci mazauna yankin da su baiwa jami’an lafiya hadin kai tare da halartar shirin domin cin gajiyar magungunan.

 

A nasa jawabin, Daraktan Kiwon Lafiyar Jama’a, Dakta Abubakar Sadiq Idris, ya jaddada kudurin gwamnatin jihar na ci gaba da yakar cututtukan da aka yi watsi da su ta hanyar shirye-shiryen kiwon lafiya da kuma hadin gwiwa da kungiyoyin tallafi.

 

A jawabin maraba, wakilin Shugaban Karamar Hukumar Kaduna ta Kudu, Dakta Maidubu, ya gode wa Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Kaduna da kuma kungiyar Sightsavers bisa tallafinsu ga wannan shiri.

 

Ya tabbatar da cewa za a raba magungunan yadda ya kamata domin tabbatar da cewa duk wadanda suka cancanta sun amfana da shirin.

 

Hakimin Tudun Wada, Alhaji Tahir Mahmud, wanda shi ne Uban Taron, ya yi alkawarin cikakken goyon bayan masarautar gargajiya domin ganin shirin ya yi nasara.

 

Ya kara da cewa za su wayar da kan al’umma tare da karfafa musu gwiwa su fito domin karbar magungunan.

 

Daya daga cikin abubuwan da suka dauki hankalin mahalarta taron shi ne wasan kwaikwayo da aka gabatar domin wayar da kan al’umma kan haddasuwar cutar, hanyoyin kariya, da kuma muhimmancin halartar shirin rabon magungunan.

Labarai

Labarai3 hours ago

NEMA Da Masu Ruwa Da Tsaki Sun Kara Haɗa Gwiwa Don Hana Aukuwar Ambaliya Da Hadarin Tankar Mai

  By Adamu Yusuf   Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA), tare da haɗin gwiwar masu ruwa da...

Labarai1 day ago

Kaduna Ta Kaddamarda Shirin Rabon Maganin Kariya Daga Cutar Dundumi

  Daga Khadija Kubau   Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Kaduna tareda haɗin gwiwar kungiyar Sightsavers sun kaddamar da shirin raba...

Ilimi1 day ago

Hukumar Ilimantar Da Makiyaya Ta Kasa Ta Horarda Ma’aikatanta Kan Yanda Za’a Mayarda ‘Ya’yan Makiyaya Makaranta 

  By Adamu Yusuf   Hukumar Ilimantar da Makiyaya Ta Kasa (NCNE) ta shirya taron horas da ma’aikatan ta kan...

Labarai2 days ago

NCAA ta Yaba wa Hukumar Alhazai ta Jihar Kebbi Bisa Kyakkyawan Tanadin Aikin Hajji

Daga Sani Dutsinma Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta Najeriya (NCAA), ta yaba da kokarin Hukumar Jin Daɗin Alhazai...

Labarai2 days ago

Sojoji Sun Kashe ’Yan Bindiga 45 a Katsina

Rundunar sojin Najeriya ta kashe ’yan bindiga 45 a wani mummunan artabu da aka yi a yankin Danmusa na cikin...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Kebbi Ta Bukaci Malamai Su Yi Wa’azin Zaman Lafiya

Gwamnatin Jihar Kebbi ta karyata zargin cewa gwamnatin Gwamna Nasir Idris ba ta taka rawar gani wajen bunkasa harkokin addinin...

Labarai2 days ago

Ranar Mata Ta Duniya: Gwamnatin Kano Ta Bukaci A Kara Tallafa wa Mata da ’Yan Mata

Kwamishinar Harkokin Mata, Yara da Masu Bukata ta Musamman ta Jihar Kano, Amina Abdullahi, ta bukaci masu ruwa da tsaki...

Labarai2 days ago

Uwargidan Gwamnan Zamfara Ta Yi Kira Da A Karfafa Mata

Uwargidan Gwamnan Jihar Zamfara, Hajiya Huriyya Dauda Lawal, ta bukaci hukumomin gwamnati, abokan hulda na ci gaba, sarakuna, malamai da...

Labarai2 days ago

’Yan Sanda Sun Kama Mutane Biyu Kan Lalata Kayan Wutar Lantarki a Nasarawa

Rundunar ’yan sandan Jihar Nasarawa ta kama wasu mutane biyu da ake zargi da lalata igiyoyi da sandunan wutar lantarki...

Labarai2 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Biyu Da Ake Zargin ’Yan Bindiga Ne a Kwara

Hukumar tsaron farin kaya ta Najeriya NSCDC a Jihar Kwara ta kama wasu mutane biyu da ake zargi da alaka...

Mafi Shahara