Labarai
Amfani da albarkatun gida zai ƙarfafa tattalin arzikin Nijeriya
Amfani da kadarorin masana’antu na ƙasa yadda ya kamata zai ƙara samun kuɗaɗen waje (foreign exchange) tare da samar da guraben ayyukan yi a Najeriya.
Wani masani kan ci gaba da tsaron ƙasa, Galadiman Ruwan Zazzau, Dakta Ja’afar Sa’ad, ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da ’yan jarida a Kaduna.
Ya nuna damuwa kan yadda ƙasar ke ci gaba da dogaro da shigo da albarkatun ƙasa daga waje, duk da cewa ana da wadatattun albarkatun cikin gida.
Dakta Ja’afar Sa’ad ya ce ci gaba da dogaro da shigo da muhimman albarkatun ƙasa daga waje na nuna wata matsala ta tsarin tattalin arziki, wadda ke rage ajiyar kuɗaɗen ƙasa tare da fallasa ƙasar ga matsalolin waje.
Galadiman Ruwan Zazzau ya jaddada cewa gazawar amfani da cikakkiyar damar da Najeriya ke da ita a cikin gida na iya ƙara tsananta matsin lambar kuɗaɗen gwamnati da kuma ƙara yawan marasa aikin yi.
Dakta Ja’afar Sa’ad ya ba da shawarar a gaggauta farfaɗo da Hukumar Samar da Kuɗaɗen Shiga ta Ƙasa da Haɗin Gwiwar Kuɗi (National Revenue Regeneration and Financial Cooperation), a matsayin wata hanya ta bunkasa tattalin arzikin ƙasa, domin mayar da tubalan masana’antu zuwa hanyoyin samar da kuɗaɗen shiga.
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai20 hours ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai22 hours ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
