Connect with us

Labarai

Rashin Wakilci Nagari: Al’ummar Kauru Sun Ce A’a ga Wa’adi na 3 na Muktar Chawai

Published

on

Siyasa na da wata hanya ta bayyana ainihin niyya ta hanyar lokaci. Taron da ɓangaren Hon. Mukhtar Zakari Chawai ya shirya kwanan nan, wanda aka sanya wa suna “APC Strategic Engagement Kauru Local Government”, ya zo ne jim kaɗan bayan suka daga jama’a kan matakinsa na neman wa’adi na uku a Majalisar Wakilai. Ga mutane da dama a Kauru, wannan taro bai yi kama da sahihin tattaunawa da al’umma ba, sai dai yunƙurin gaggawa na rage tasirin ƙorafin da ke ƙara ƙamari a tsakanin jama’a.

Duk wani bincike ya nuna cewa taron ya fi kama da haɗuwar tsofaffin ’yan siyasa da abokan hulɗar kafafen sadarwa ta zamani, ba mu’amala ta gaskiya da al’ummar Kauru ba.

A tsarin dimokiraɗiyya, wannan bambanci yana da muhimmanci. Ana iya shirya taruka, a fitar da sanarwa, a bayyana biyayya, amma a ƙarshe ƙuri’u na jama’a a ƙauyuka, unguwanni da rumfunan zaɓe ne ke yanke hukuncin zaɓe.

Babban saƙon da aka riƙa jaddadawa a taron shi ne nuna cikakkiyar biyayya ga Gwamna Uba Sani da Shugaba Bola Ahmed Tinubu. Babu shakka, biyayya ga shugabancin jam’iyya abu ne da ake tsammani. Sai dai biyayya kaɗai ba ta lashe zaɓe. Abin da ke lashe zaɓe shi ne amincewa, kuma amincewa tana samuwa ne ta hanyar aiki, kusanci da jama’a, da girmama ra’ayin masu zaɓe.

Mutanen Kauru ba sa adawa da jam’iyyar APC, haka nan ba sa adawa da gwamna. Abin da suke adawa da shi, shi ne goyon bayan shugabanci da suke ganin ba wakilce su yadda ya kamata ba.

Zaɓen Majalisar Wakilai na shekarar 2023 har yanzu yananan sabo a zukatan jama’a. A wancan zaɓe, Hon. Mukhtar Chawai bai yi nasara a rumfunan zaɓe ba, inda aka dankarashi da kasa da tazara mai yawa, kusan ƙuri’u 5,000, abin da ya nuna yanayin ra’ayin jama’a a wancan lokaci. Duk da cewa samun kujerarsa ta hannun kotu na iya kammala shari’a, bai goge ainihin gaskiyar siyasa ba. Har yanzu jama’a da dama na jin cewa an juya musu sakamakon zaɓensu, kuma wannan ra’ayi ya ci gaba da tasiri kan tunanin al’umma.

Lokacin da mutum ya hau mulki a irin wannan yanayi, tsammanin jama’a kan kasance babba. ’Yan mazaba sukan sa ran ganin aiki a fili, tsayawa tsayin daka wajen kare muradun yankin, da kuma amfanin da zai shafi al’umma kai tsaye. Abin takaici, yawancin mutanen Kauru na ganin da wahala su nuna manyan ayyuka, wakilci mai tasiri, ko kuma ci gaba da hulɗa da jama’a da za su ba da hujjar tsawaita wa’adi. Wannan tazara tsakanin tsammani da abin da aka gani ita ce ke haddasa ƙara yawan fushin jama’a a faɗin ƙaramar hukumar.

A jihar Kaduna da ma Najeriya baki ɗaya, akwai misalai bayyanannu da ke nuna cewa ingantaccen wakilci ba ya dogara da shekaru ko dogon zama a siyasa. Matasa ’yan majalisa irin su Bello El-Rufai sun nuna cewa kusanci da jama’a, jawo ayyuka masu ma’ana, da sanar da al’umma ci gaban aiki akai-akai abu ne mai yiyuwa cikin ɗan gajeren lokaci. Irin waɗannan misalai suna sa jama’a kasa karɓar uzurin gazawa.

Dalilin nan ne ya sa yunƙurin neman wa’adi na uku ke tayar da ƙarin damuwa. Neman ƙarin wa’adi ba laifi ba ne a kansa, amma dole ne ya kasance tare da manyan nasarori da karuwar amincewar jama’a. Idan babu waɗannan, irin wannan buri yana fara bayyana a matsayin son rai na kai, ba hidimar jama’a ba. Mutanen Kauru na tambaya guda mai muhimmanci: “Me ya sauya tun bayan 2023 da zai ba da hujjar sabon wa’adi?”

Ƙoƙarin jingina kai sosai da gwamna shi ma yana tayar da tambayoyi a tsakanin masu zaɓe. Gwamnoni sukan yi nasara ne idan sun yi aiki tare da ’yan takara masu cikakken goyon bayan jama’a. Jingina kai da wanda jama’a ke ganin sun ƙi a rumfunan zaɓe na iya zama barazana ta siyasa. Mutanen Kauru suna da wayewar siyasa, kuma sun saba bayyana matsayinsu a fili ta hanyar ƙuri’a.

Wannan rubutu ba hari ba ne ga Gwamna Uba Sani. Saƙo ne na gaskiya daga Jakadun Matasa na Kauru (KYA). Idan gwamnan na son samun nasara a ƙaramar hukumar Kauru, ya kamata ya saurari jama’a kai tsaye, ba kawai ta bakin ’yan siyasa masu shiga tsakani ba. Shawarwari na gaskiya a dukkan unguwanni da ƙauyuka za su tabbatar da yanayin ra’ayin jama’a. Abin da mutane ke so shi ne wakilci nagari, mai amsa kiran jama’a, kuma wanda ya fifita muradun al’umma.

Dimokiraɗiyya ta fi hukuncin kotu da tarukan jam’iyya. Ana gina ta ne kan yardar jama’a da amincewarsu. Idan shugabanni suka manta da wannan gaskiya, sukan rasa jama’a. Mutanen Kauru sun riga sun bayyana matsayinsu, kuma alamu na nuna suna shirye su sake yin hakan.

A ƙarshe, iko ba ya fitowa daga kusanci da masu mulki, yana fitowa ne daga jama’a. Ana iya bayyana biyayya a taruka, amma amincewa sai an samu ta a rumfunan zaɓe. Wannan ita ce gaskiyar da Kauru ke ci gaba da tabbatarwa.

Yusuf Zubairu/Junaidu Ishaq Maisalari 

Labarai

Labarai4 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi5 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai6 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai6 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai6 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai6 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai6 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai6 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Ilimi7 days ago

Zamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta

Daga Aminu Dalhatu  Hukumar Ilimin Bai-daya ta Jihar Zamfara, ZSUBEB, ta kaddamar da shirin shigar da yara makaranta na shekarar...

Labarai7 days ago

Gwamnan Kebbi Ya Yabi WAMY Kan Jinya Kyauta Ga Marasa Lafiya

Daga Sani Dutsinma Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya yaba wa Ƙungiyar Matasa Musulmi ta Duniya (WAMY) kan shirya aikin...

Mafi Shahara