Labarai
Eid El-Fitr: Sarkin Kauru Ya Jaddada Muhimmancin Hadin Kai da Zaman Lafiya a Tsakanin Al’umma
Daga Yusuf Zubairu
Sarkin Kauru, Zakari Ya’u Usman na biyu, ya yi kira ga al’ummar masarautar da ke Jihar Kaduna, da su ci gaba da tabbatar da haɗin kai, da zaman lafiya yayin gudanar da bukukuwan Sallah .
Sarkin ya yi wannan kira ne a sakon sa na Sallah da ya gabatar a ranar Juma’a, 20 ga watan Maris na shekarar 2026, bayan kammala azumin watan Ramadan.
Ya gode wa Allah bisa bai wa Musulmi damar ganin wannan lokaci cikin ƙoshin lafiya da walwala.
Dangane da tsaro, Sarkin ya tabbatar da cewa an samu ci gaba a yankin, amma ya yi gargadin har yanzu akwai barazanar satar mutane da sauran laifuka makamantansu.
Ya bukaci al’umma da su kasance masu lura don kare yankunansu, tare da kai rahoton duk wani motsin bako a yankin.

Muhammad Sani Suleiman (Danburan)
Zakari Ya’u II ya jaddada muhimmancin haɗin kai tsakanin dukkan al’umma, ba tare da la’akari da addini ko kabilanci ba, yana mai cewa haɗin kai ne ke tabbatar da zaman lafiya da tsaro a masarautar.
Sarkin yakuma bayyana zaman lafiya a matsayin ginshiƙin ci gaba, inda ya yi gargadi kan yada jita-jita da ka iya haifar da tashe tashen hankula.
Ya kuma bukaci al’summar masarautar da su ci gaba da zama tare cikin mutunta juna da fahimtar juna.
Har ila yau, Sarkin ya jaddada muhimmancin kula da lafiyar jama’a, inda ya bukaci su kula da tsafta, tsaftace muhalli, da kuma neman kulawar lafiya cikin gaggawa idan bukatar hakan ta taso.
Haka zalika ya yi nuni da muhimmancin rigakafin cututtuka, ciki har da allurar rigakafi na yau da kullum, musamman ga yara da mata masu juna biyu, bisa shirye-shiryen lafiyar jama’a da ake gudanarwa.

A bangaren ilimi, Sarkin Kauru ya bukaci a kara himma a fannin ilimin zamani da na addini, yana mai kira ga iyaye da matasa su fifita neman ilimi a matsayin ginshiƙin ci gaban al’umma.
Ya kuma ba da shawarar dogaro da kai, musamman ga matasa, inda ya bukace su da su koyi sana’o’i maimakon jiran aikin gwamnati kawai, yana mai cewa yakamata arika amfani da shirye-shiryen gwamnati kamar na ƙungiyoyin manoma yadda ya kamata.
Sarkin ya yaba wa Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, bisa kokarinsa na kawo ci gaba a yankin, ciki har da gina hanyoyi, shirin inganta wutar lantarki, da matakan ƙarfafa tsaro. Haka kuma ya yaba wa Shugaban Karamar Hukumar Kauru, Honarabul Bashir Tanko Dawaki, bisa jajircewarsa wajen ci gaban karkara.
Ya bukaci gwamnati ta kara himma wajen ciki gina muhimman hanyoyi da za su haɗa Kauru da sauran yankuna makwabta, da ƙarin tallafin noma ga manoma, da kuma kafa makarantar sakandare a garin Kauru.
Zakari Ya’u II ya kuma yi kira da a ci gaba da aikin gyaran Fadar Masarautar Kauru, musamman mataki na biyu.
A ƙarshe, Sarkin ya yi addu’ar samun zaman lafiya yayin bukukuwan Sallah, da ci gaba da lafiya, tare da roƙon Allah ya karɓi ibadun da aka yi a watan Ramadan.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
