Labarai
Gwamnatin Jigawa Za ta Dauki Sabbin Ma’aikata a Kananan Hukumomi
Daga Usman Muhammad Zaria
Gwamnatin Jihar Jigawa ta dage takunkumin daukar ma’aikata bisa barazanar karancin ma’aikata a kananan hukumomi 27 na jihar.
Shugaban Hukumar Kula da Ayyukan Kananan Hukumomi ta Jihar Jigawa, DIG Uba Bala Ringim mai ritaya ne ya bayyana hakan a ranar Laraba yayin da yake wa ‘yan jarida bayani kan nasarorin da hukumar ta cimma a shekarar 2025, a dakin taro na hukumar.

Ringim ya ce an dauki matakin ne sakamakon raguwar ma’aikata da aka samu a kananan hukumomi da Hukumar Ilimi ta Kananan Hukumomi (LEAs), wanda yawanci ya faru ne saboda ritaya da kuma rasuwa.
Ya bayyana cewa a shekarar 2025 kadai, hukumar ta yi wa ma’aikata 1,682 karin girma tare da shirya taruka da bitoci 163 da nufin karfafa kwarewa, ingancin aiki a matakin kananan hukumomi.
A cewarsa, ma’aikata 628 sun yi ritaya daga aiki a cikin shekarar a fadin kananan hukumomi, yayin da ma’aikata 72 na kananan hukumomi da 83 na hukumar ilimi suka rasu. Bugu da kari, ma’aikatan hukumar ilimi na kananan hukumomi 704 ma sun yi ritaya a wannan lokaci.

“Yawaitar ritaya ba tare da gaggauta maye gurbi ba na ci gaba da raunana karfin tafiyar da mulki a kananan hukumomi,” in ji Ringim.
Ya bayyana cewa a halin yanzu hukumar na da ma’aikata 6,322, wanda ke nuna raguwar kusan kashi ashirin bia dari, sakamakon ritaya da rasuwa a shekarar 2025.
Ringim ya kara da cewa Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da daukar karin ma’aikatan kananan hukumomi a shekarar 2026 domin karfafa yawan ma’aikata da inganta isar da ayyuka ga al’umma a fadin kananan hukumomin jihar.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
