Labarai
Ranar Mata Ta Duniya: Gwamnatin Kano Ta Bukaci A Kara Tallafa wa Mata da ’Yan Mata
Kwamishinar Harkokin Mata, Yara da Masu Bukata ta Musamman ta Jihar Kano, Amina Abdullahi, ta bukaci masu ruwa da tsaki su kara kaimi wajen tallafa wa mata da ’yan mata a fadin jihar.
Ta bayyana hakan ne yayin bikin Ranar Mata ta Duniya, inda ta ce bikin na tunatar da muhimmiyar rawar da mata ke takawa wajen gina iyali, al’umma da kuma ci gaban kasa.
Kwamishinar ta jaddada kudurin ma’aikatar wajen inganta daidaito tsakanin maza da mata, kare hakkin mata da yara, da kuma samar da damar da za ta ba mata damar cimma burinsu.
Ta kuma yabawa Gwamna Abba Kabir Yusuf kan goyon bayan manufofi da shirye-shiryen da ke karfafa mata da kuma kula da marasa karfi a Kano.
A karshe, ta bukaci iyalai da kungiyoyi su kara tallafa wa shirye-shiryen ilimi, kasuwanci da jagoranci ga mata, domin gina al’umma mai adalci inda kowa zai samu dama ba tare da wariya ba.
Khadijah Aliyu/Kano
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai1 day ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai1 day ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
