Labarai
KAROTA Ta Sha Alwashin Ƙara Ƙarfafa Haɗin Kai da Jami’an Soji a Jihar Kano
Daga Khadijah Aliyu
Shugaban Hukumar Kula da Hanyoyi da Tsaron Ababen Hawa ta Jihar Kano, (KAROTA), Faisal Mahmud Kabir, ya sake jaddada kudirinsa na inganta dangantaka mai kyau da haɗin kai da rundunonin soji da ke aiki a jihar Kano.
Faisal Mahmud ya sha alwashin hakan ne yayin da ya karɓi baƙuncin Kwamandan 403 na makarantar horar da matukan jiragen sama da ke Kano, Group Captain Uchenna Ihediwa, a hedikwatar KAROTA.
Shugaban na KAROTA ya amince cewa a wasu lokuta ana samun rashin fahimta tsakanin jami’an KAROTA da jami’an soji, amma ya tabbatar da cewa hukumar na aiki domin samar da hanyoyin warware duk wata takaddama cikin lumana.
Ya jaddada cewa burinsu shi ne tabbatar da kyakkyawar alaƙar aiki wadda za ta amfani jami’an tsaro da kuma al’umma baki ɗaya.
A nasa jawabin, Group Captain Uchenna Ihediwa ya ce ziyarar na da nufin ƙarfafa haɗin gwiwar da ke akwai tsakanin KAROTA da makarantar horas da matukan jiragen sojin sama, tare da mai da hankali kan tabbatar da doka da oda a hanyoyin jihar.
Ya jaddada muhimmancin haɗin kai, ƙwarewa, da kuma tsayawa tsayin daka ga dukkan jami’an tsaro domin tabbatar da kula da zirga-zirgar ababen hawa.
Kwamandan ya yabawa jami’an KAROTA bisa jajircewarsu da ƙwazon aikinsu, inda ya nuna buƙatar ci gaba da haɗin gwiwa tsakanin hukumomi domin inganta tsaron jama’a da kuma tabbatar da bin dokokin zirga-zirga.
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai20 hours ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai22 hours ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
