Labarai
Tinubu Ya Nada Gwamna Uba Sani Jakadan Shirin Renewed Hope
Daga Bello Wakili
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da nadin Gwamnan Jihar Kaduna Sanata Uba Sani, a matsayin jakadan shirin sabunta kudurori na Renewed Hope kuma mataimakin darakta mai kula da ayyukan jam’iyya da wayar da kai.
Sanarwan hakan ta fito ne daga Fadar shugaban kasa inda ta ce an yi nadin ne bisa la’akari da shugabanci nagari da gwamna Uba Sani ke gudanarwa.
Shugaban kasa Tinubu a matsayinsa na shugaban jam’iyyar APC, ya bukaci gwamnan Kaduna ya taimakawa jam’iyyar wurin wayar da kai da bullo da tsare-tsare a kasa baki daya.
Sanarwan ta ce a matsayinsa na jakadan shirin sabunta kudurori kuma mataimakin darakta, ana sa ran zai kasance kafada-da-kafada da darakta janar na jakadan shirin sabunta kudurori da shugabanin jam’iyyar APC musamman shugaban jam’iyyar APC na kasa, wurin bunkasa dama da daidaito da tsare-tsare a tsakanin ‘ya’yan jam’iyyar a kowane mataki.
-
Labarai2 days agoIran ta Tabbatar da Kisan Ayatollah Khamenei a Hare-haren Amurka da Isra’ila
-
Labarai4 days agoMajalisar Dokokin Jihar Kaduna Ta Amince da Kasafin Kudin Kananan Hukumomin Jihar na 2026
-
Labarai4 days agoAzumin Ramadan: Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kudu Ya Bada Tallafin Kudi ga Marasa Galihu
-
Labarai6 days agoUwargidan Gwamnan Zamfara Ta Kaddamar da Rabon Tallafin Ramadan ga Marasa Galihu
-
Labarai6 days agoWani Bam Kirar Hannu Ya Fashe a Kan Hanyar Gusau Zuwa Funtua
-
Labarai3 days agoBankin Raya Kasashen Afirka Zai Samar da Shirin Bunƙasa Aikin Noma a Jigawa
-
Labarai3 days agoGwamnatin Jigawa ta Gargadi ‘Yan Kwangila Kan Ingancin Abincin Ramadan
-
Labarai3 days agoMasarautar Hadejia ta Raba Zakkar Kayan Amfanin Gona da Dabbobi a Garin Unik
