Labarai
Uwargidan Gwamnan Zamfara Ta Kaddamar da Rabon Tallafin Ramadan ga Marasa Galihu
Daga Aminu Dalhatu
Uwargidan Gwamnan Zamfara, Hajiya Huriyya Dauda Lawal, ta kaddamar da shirin rabon kayan abinci na watan Ramadan na bana.
Wannan ce shekara ta uku a jere na tallafin jin kai ga gidaje marasa galihu a fadin jihar.
An gudanar da bikin kaddamarwar ne a karamar hukumar Shinkafi, inda aka fara rabon kayan abincin, wanda iyalai 50,000 daga mazabu 147 da ke fadin jihar za su amfana.
A cewar Hajiya Huriyya, shirin na nuna kudirin gwamnati na tabbatar da cewa iyalai marasa karfi sun gudanar da ibadar watan Ramadan cikin kwanciyar hankali da walwala.

A cikin wata sanarwa da Sakatariyar Yada Labarai ta Uwargidan Gwamnan, Rabi Yusuf, ta fitar, ta ce an tsara shirin ne a matsayin wani mataki na rage radadin matsin tattalin arziki tare da karfafa tallafin jin kai ga marasa galihu a lokacin azumi.
Kowane kunshin kayan abincin ya kunshi muhimman kayayyaki da suka hada da kilo 20 na shinkafa, kilo biyar-biyar na wake, sukari, gero da masara, sai gishiri, man girki, taliya da kuma atamfofi.
Domin tabbatar da gaskiya da rikon amana, an kafa kwamitocin rabon kayayyakin a matakin mazabu a fadin jihar, inda suke aiki tare da hukumomin kananan hukumomi da shugabannin al’umma domin tabbatar da kayan sun kai ga wadanda suka dace.

Uwargidan Gwamnan ta gargadi mambobin kwamitocin da su yi aiki bisa gaskiya da adalci, tare da godiya ga Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, bisa shugabancinsa na tausayi da kula da jama’a, inda ta jaddada cewa gwamnatin sa na ci gaba da ba da muhimmanci ga jin dadin marasa.
A ci gaba da wannan aiki, Uwargidan Gwamnan ta kai ziyara wasu al’ummomi a masarautun Shinkafi, Bazai, Kaura Namoda da Zurmi, inda ta raba karin tallafin kayan Ramadan da na Sallah da kanta.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
