Connect with us

Labarai

‘Yan Sanda Sun Ceto Yara Mata 28 Da Aka Sace A Katsina

Published

on

Rundunar ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro sun ceto ‘yan matan nan  28 da aka sace daga kauyen Kasai da ke karamar hukumar Batsari a jihar Katsina.

A wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Abubakar Sadiq ya sanya wa hannu, ta ce an kubutar da dukkan ‘yan matan ba tare da wani rauni ba.

‘Yan fashin sun yi wa yaran ‘yan shekara takwas zuwa sha biyar kwanton bauna ne a bayan gari, inda suka je dibar itacen da za su kai gida domin yin girki.

Sanarwar ta ce da samun rahoton faruwar lamarin, kwamishinan ‘yan sandan jihar, Aliyu Abubakar, ya tura jami’ai zuwa dajin tare da yin tattaki domin ceto yaran.

Ya yi bayanin cewa ‘yan bindigar sun yi watsi da yaran ne sakamakon matsin lamba da ‘yan sanda suka yi musu, inda suka gudu suka bar  yaran wadanda a halin yanzu suke cikin koshin lafiya.

Kokarin hadin gwiwa da tawagar ceto ta sa kai, tare da dabarun da rundunar ta dauka, ya sa aka sako dukkan wadanda aka sace”. Inji shi.

“Wannan nasara ta nuna jajircewar rundunar da kuma duk wanda ke da hannu acaiki.n ceton.

Sanarwar ta kara da cewa “Za a ci gaba da kokarin tabbatar da  tsaron al’umma da jihar baki daya.

 

Ismai’l Adamu

Labarai

Labarai4 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi5 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai6 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai6 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai6 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai6 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai6 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai6 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Ilimi7 days ago

Zamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta

Daga Aminu Dalhatu  Hukumar Ilimin Bai-daya ta Jihar Zamfara, ZSUBEB, ta kaddamar da shirin shigar da yara makaranta na shekarar...

Labarai1 week ago

Gwamnan Kebbi Ya Yabi WAMY Kan Jinya Kyauta Ga Marasa Lafiya

Daga Sani Dutsinma Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya yaba wa Ƙungiyar Matasa Musulmi ta Duniya (WAMY) kan shirya aikin...

Mafi Shahara