Connect with us

Ilimi

Gwamnatin Nasarawa Ta Roki Malaman Jami’o’i Masu Yajin Aiki Su Koma Aji – SSA Ahemba

Published

on

Gwamnatin Jihar Nasarawa ta yi kira ga malaman manyan makarantu mallakar jihar da ke yajin aiki da su janye yajin aikin da suke gudanarwa, domin bai wa tattaunawa damar ci gaba don warware matsalolin da ke haddasa rikicin cikin gaggawa.

Babban Mataimaki na Musamman ga Gwamna Abdullahi Sule kan Harkokin Jama’a, Mista Peter Ahemba, ne ya yi wannan roko yayin da yake jawabi ga ’yan jarida a taron manema labarai na watanni biyu-biyu da aka gudanar a Lafia, babban birnin jihar.

Mista Ahemba ya ce yajin aikin da Malaman Kwalejin Ilimi ta Akwanga da kwalejin kimiyya da fasaha ta Isa Mustapha Agwai Lafia, da Kwalejin Aikin Noma, Kimiyya da Fasaha ta Lafia ke yi na iya kawo cikas ga karatun dalibai. Saboda haka, ya roki ƙungiyoyin malaman da su koma teburin tattaunawa domin cimma matsaya cikin lumana.

Ƙungiyoyin Malaman Manyan Makarantu na Jihar Nasarawa sun ayyana yajin aikin sai baba-ta-gani a ranar 29 ga Disamba, 2025, bisa rashin aiwatar da sabon mafi ƙarancin albashi na ƙasa ga mambobinsu.

Babban Mataimakin na Musamman ya bayyana cewa kwanan nan Gwamna Abdullahi Sule ya raba katifa dubu ɗaya da gadaje ga daliban Kwalejin Ilimi ta Akwanga (COEA), domin inganta muhallin koyo da koyarwa.

Ya ce wannan rabon na daga cikin kulawar da gwamnatin Gwamna Abdullahi Sule ke bai wa fannin ilimi tun daga lokacin da ta hau mulki a shekarar 2019.

Mista Ahemba ya ƙara da cewa gwamnatin ta gina azuzuwa da dama, ta gyara makarantu masu yawa, tare da gina katangar kariya a makarantu da dama domin kare su daga mamaya.

Ya kuma ce gwamnatin ta fahimci yadda wasu miyagun mutane ke shiga jihar a hankali, lamarin da ke barazana ga tsaron mazauna yankin.

Mista Ahemba ya yi Allah-wadai da kakkausar murya kan harin tsakar dare da wasu da ba a tantance su ba suka kai wa mazauna Akunza da ke yankin Ashige a karamar hukumar Lafia.

Ya tabbatar wa al’umma cewa gwamnati na aiki kafada da kafada da hukumomin tsaro da sauran masu ruwa da tsaki wajen aiwatar da sabbin matakan tsaro domin shawo kan irin waɗannan hare-hare.

Ya kuma yi kira ga ’yan ƙasa da su rika bai wa hukumomin tsaro sahihan bayanai da za su taimaka wajen kama masu aikata laifuka a dukkan sassan jihar.

Mista Ahemba ya tabbatar wa jama’a cewa gwamnati na yin duk mai yiwuwa domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

Saboda haka, ya roki jama’a da su rika kai rahoton duk wani abu da suke zargin ba daidai ba ga hukumomin da suka dace, tare da ba da cikakken haɗin kai ga jami’an tsaro domin hana aikata laifuka da yaki da su.

COV: Aliyu Muraki / Lafia

Labarai

Labarai6 hours ago

Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu

Daga Nasir Malali  Dakarun Sashe na biyu na Rundunar Haɗin Gwiwa ta Arewa maso Yamma, Operation FANSAN YAMMA, sun ceto...

Labarai9 hours ago

NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta

Daga Yusuf Zubairu, Kaduna Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Yamma ta bayyana dawo da tsaro a matsayin babban fifikonta a...

Labarai5 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi5 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai6 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai7 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai7 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai7 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai7 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai7 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Mafi Shahara