Labarai
Shugaba Tinubu Ya Gabatar da Kasafin 2026 a Gaban Majalisa
Daga Bello Wakili
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya gabatar da kasafin kuɗin shekarar 2026 da ya kai Naira Tiriliyan 58.18 ga zaman haɗin gwiwa na Majalisar Dokoki ta Ƙasa, inda ya bayyana shi a matsayin “Kasafin Ƙarfafa Ci gaba, Sabunta Juriya da Wadata ga Kowa.”
Da yake jawabi ga ’yan majalisa a Abuja, Shugaban ya ce Dokar Kasafin Kuɗi ta 2026 ta ginu ne bisa sauye-sauyen tattalin arziki da aka aiwatar cikin shekaru biyu da rabi da suka gabata, waɗanda suka mayar da hankali kan daidaita tattalin arziƙin ƙasa, karfafa masu zuba jari, da shimfiɗa tubalin ci gaba mai amfani ga kowa.
Shugaba Tinubu ya tsara kashe naira tiriliyan 15.25 domin gudanar ayyukan yau da kullum na gwamnati, sannan ya ware naira tiriliyan 26.08 domin gudanar da manyan ayyuka da more rayuwa a ƙasar.
Tinubu ya tsara kasafin ne a bisa hasashen farashin gangar ɗanyen man fetur a kan dala 64.85.
Haka an yi hasashen sama da gangar ɗanyen man fetur miliyan 1.84 a kullum, sannan ya ayyana canjin dala a kan naira 1,400.
Ma’aikatun da suka fi samun kasafi su ne Ma’aikatar Tsaro, inda za ta sami Naira tiriliyan 5.41, sai ababen more rayu, inda za a kashe Naira tiriliyan 3.56, yayin da Ma’aikatar Ilimi za ta kaishe Naira Tiriliyan 3.52, sai Ma’aikatar Lafiya kuma za ta kashe Naira tiriliyan 2.48.
Tinubu ya ce tsaro shi ne ginshiƙin ci gaba, inda ya sanar da sake fasalin tsarin tsaron ƙasa da kuma sabon tsarin yaƙi da ta’addanci.
A fannin ilimi kuwa, Shugaban ya bayyana faɗaɗa Shirin Lamunin Ilimi na Ƙasa (NELFUND), wanda ya tallafa wa sama da dalibai 788,000 a manyan makarantu 229.
Yayin gabatar da Dokar Kasafin Kuɗi, Tinubu ya nemi haɗin kai tsakanin ɓangaren zartarwa da majalisa, yana mai cewa “Da haɗin kai da jajircewar al’ummar Najeriya, za mu cika dukkan alkawarin Ajandar Sabunta kudurori (Renewed Hope Agenda),” in ji shi.
-
Labarai5 days agoRanar Mata Ta Duniya: Gwamnatin Kano Ta Bukaci A Kara Tallafa wa Mata da ’Yan Mata
-
Labarai5 days agoGwamnatin Kebbi Ta Bukaci Malamai Su Yi Wa’azin Zaman Lafiya
-
Labarai5 days agoSojoji Sun Kashe ’Yan Bindiga 45 a Katsina
-
Labarai6 days agoGwamnatin Zamfara Ta Ayana Dokar Ta-baci Kan Shan-Inna a Karamar Hukumar Gummi
-
Labarai5 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Biyu Da Ake Zargin ’Yan Bindiga Ne a Kwara
-
Labarai5 days agoNCAA ta Yaba wa Hukumar Alhazai ta Jihar Kebbi Bisa Kyakkyawan Tanadin Aikin Hajji
-
Labarai2 days agoAn Nada Kabir Yahaya Darakta Janar na Farko na Filin Jirgin Sama da ke Gusau
-
Labarai5 days ago’Yan Sanda Sun Kama Mutane Biyu Kan Lalata Kayan Wutar Lantarki a Nasarawa
