Connect with us

Labarai

An Yi Wa Jami’an FRSC A Jos Gwajin Idanu Kyauta Domin Ranar Glaucoma Ta Duniya

Published

on

Jami’an kula da hanya na Hukumar Kiayyae hadura ta kasa a Jos sun samu damar yin gwajin idanu da kuma samun magani kyauta kan cutar Glaucoma ko kuma dundumi, a wani bangare na bukukuwan Ranar Glaucoma ta Duniya ta bana.

Da take jawabi a wajen shirin, ƙwararriyar likitar ido a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jos Farfesa Perpetua Udogbo, ta bayyana cewa jami’an FRSC na iya taka muhimmiyar rawa wajen rage hadurran mota a kan tituna ta hanyar tabbatar da cewa direbobin da ke tuka ababen hawa suna da lafiyayyen gani.

Wakilinmu Josiah Buzun ya ruwaito cewa an gudanar da gwajin ne a hedikwatar FRSC da ke kan titn Zaria a Jos, da kuma ofishin su na Bukuru, domin sauƙaƙa wa mahalarta samun damar halartar shirin.

Shirin wani bangare ne na ayyukan da ake gudanarwa domin bikin Makon Glaucoma na Duniya, wanda ƙungiyar Sight Savers International ta dauki nauyi tare da haɗin gwiwar Health and Development Support Programme (HANDS), Christian Blind Mission, da kuma Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Filato.

Ko da yake an shirya gwajin ne musamman ga jami’ai da ma’aikatan FRSC, wasu mazauna yankin sun kuma yi amfani da damar domin a duba idanuwansu domin gano ko suna dauke da cutar.

Farfesa Udogbo ta yi kira ga a ƙara ƙarfafa haɗin gwiwa da FRSC domin tabbatar da cewa direbobin da ke tuka ababen hawa a kan tituna suna da lafiyayyen gani kafin a ba su damar yin tuƙi.

Ta kuma jaddada muhimmancin yin gwajin cutar da wuri domin gano ta da kuma fara magani cikin lokaci, tana mai cewa Glaucoma cuta ce mai hatsari wadda kan iya janyo makanta a lokacin da mutum ke cikin shekarun aiki, lamarin da kan rage ingancin rayuwa tare da haddasa matsin lamba a zuciya.

Farfesa Udogbo ta bayyana cutar Glaucoma a matsayin irin hawan jini na ido, inda matsin da ke cikin ido ke karuwa har ya iya lalata jijiyoyin gani.

Sai dai ta ce idan an gano cutar da wuri, ana iya rage matsin da ke cikin ido ta hanyar magunguna, amfani da wasu kwayoyi ko kuma yin tiyata.

Mukaddashin Shugaban Kwamitin Lafiyar Ido na Jihar Filato, Dakta Rwang Pam Haruna, ya ce sun zabi gudanar da wannan gwaji ga jami’an FRSC ne saboda muhimmiyar rawar da suke takawa wajen tabbatar da tsaron hanya.

Shi ma Kwamandan Yanki na FRSC ya yaba da wannan shiri, yana mai cewa wani muhimmin mataki ne da ke taimakawa rayuwar dan Adam.

Daga cikin abubuwan da suka fi daukar hankali a wajen taron har da yin gwajin lafiya kyauta, inda aka raba magunguna da tabarau ga wadanda aka gano suna bukata.

Josiah Buzum/Jos

Labarai

Labarai4 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi5 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai6 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai6 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai6 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai6 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai6 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai6 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Ilimi7 days ago

Zamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta

Daga Aminu Dalhatu  Hukumar Ilimin Bai-daya ta Jihar Zamfara, ZSUBEB, ta kaddamar da shirin shigar da yara makaranta na shekarar...

Labarai7 days ago

Gwamnan Kebbi Ya Yabi WAMY Kan Jinya Kyauta Ga Marasa Lafiya

Daga Sani Dutsinma Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya yaba wa Ƙungiyar Matasa Musulmi ta Duniya (WAMY) kan shirya aikin...

Mafi Shahara