Labarai
Matashi Mai Digiri Na Farko Na Sayar Da Ruwan Leda A Taraba
Wani matashi mai digirin na 2 a fannin Ilimin (Theology) kuma wanda ya kammala karatun Physics, mai suna Hilekann Eric, na yawo a titunan garin Jalingo, babban birnin Jihar Taraba, yana sayar da ruwan leda domin neman abin dogaro.
Ana ganin Eric yana ɗauke da kwandon ruwan leda a kansa yana kira ga masu wucewa a kan titi yana cewa, “Pure water! Ice cold! Uku na naira 100!” yayin da rana ke tsananin duka a kansa.
Lamarin ya sha bamban da irin nasarorin ilimi da ya samu a baya.
An gano Eric ne a yankin Roadblock lokacin da wakilinmu ke tattaunawa da jama’a kan aikin sake gina Gadar Namnai da Gwamnatin Tarayya ke yi.
Eric, wanda ya fito daga al’ummar Chanchanji a ƙaramar hukumar Takum ta Jihar Taraba, ya bayyana takaicinsa kan halin da yake ciki.
“Ina da digirin digirgir biyu, amma ga ni a kan titi ina sayar da ruwan leda saboda babu aikin yi. Ina ta aiki tukuru, amma duk da haka kamar ba komai na ke yi ba,” in ji shi cikin damuwa.
Ya ce rashin aikin yi na daga cikin dalilan da ke haifar da tashe-tashen hankula da aikata laifuka a wasu wurare.
“Idan gwamnati za ta duba halin da matasa ke ciki ta tallafa musu, za su iya zama mutane masu amfani ga al’umma. Akwai mutane da za su iya kafa masana’antu ɗaya ko biyu a wannan yanki domin a ɗauki matasa aiki,” in ji Eric.
Ya ƙara da cewa shi ba shi kaɗai ba ne cikin irin wannan hali, domin akwai ɗimbin matasa masu digiri da ba su da aikin yi.
“Wannan ruwan da kuke gani ina sayarwa shi ne abin da nake rayuwa da shi. Ina gode wa Allah da haka, domin ya fi na shiga sata ko wani abu na haram,” in ji shi.
Eric ya kuma bayyana cewa wasu ’yan siyasa na amfani da matasa wajen yaƙin neman zaɓe, amma bayan sun samu mulki ba su samar musu da aikin yi ba.
A cewarsa, duk da cewa gwamnati ba za ta iya ɗaukar dukkan marasa aikin yi aiki ba, kafa masana’antu kaɗan zai taimaka wajen rage matsalar.
Sai dai ya yaba wa Gwamnatin Tarayya kan bayar da kwangilar sake gina Gadar Namnai da ta rushe, yana mai cewa wannan wani muhimmin mataki ne.
Sai dai ya nuna damuwa kan hanyar zuwa ƙaramar hukumar Kurmi a jihar Taraba, wadda ya ce ta daɗe tana cikin mummunan hali amma har yanzu ba a gyara ta ba.
“Ba wai babu manyan mutane a yankin ba, akwai su. Amma har yanzu ba su gyara hanyar ba, sai dai su riƙa amfani da ita wajen yaudarar jama’a a lokacin yaƙin neman zaɓe,” in ji shi.
A halin yanzu, Hilekann Eric na ci gaba da sayar da ruwan leda tare da fatan wata rana al’amuransa za su canza.
Ya kuma bar lambar wayarsa ga duk wanda zai iya taimaka masa: 08120231338
Sani Sulaiman
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
