Labarai
Mataimakin Gwamnan Zamfara Ya Yi Rijista a Jam’iyyar APC
Mataimakin Gwamnan Jihar Zamfara, Malam Mani Malam Mummuni, ya yi rijista a hukumance a matsayin cikakken ɗan jam’iyyar APC.
An gudanar da rajistar ne a Fadar Gwamnatin Jihar Zamfara da ke Gusau, jim kaɗan bayan kaddamar da wani taron horaswa na kwanaki biyu kan rijistar ’yan jam’iyya a dukkanin ƙananan hukumomi 14 da kuma gundumomi na jihar.
Da yake jawabi a wajen taron, Mataimakin Gwamnan ya ce muhimmancin wannan horo ba zai misaltu ba.
A cewarsa, an zaɓi mahalarta taron ne da kulawa domin su zama masu horaswa da kuma masu jagorantar aikin rijistar ’yan jam’iyya a ƙananan hukumominsu da gundumominsu.
“Kamar yadda kowa ya sani, jam’iyyarmu na ci gaba da karɓar sababbin mambobi da dama a faɗin jihar. Don haka yana da matuƙar muhimmanci tsarin rijistar ’yan jam’iyya ya kasance mai tsari, gaskiya da kuma kulawa ta yadda ya dace,” in ji shi.
Malam Mani ya yabawa Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, kan ƙoƙarinsa na ci gaba da bunƙasa jam’iyyar.
Ya kuma jaddada cewa yayin da ƙarin jama’a ke ci gaba da rungumar manufofin jam’iyyar tare da shiga cikinta, ya zama dole a samar da ingantaccen kundin rajistar mambobi wanda zai nuna ainihin ƙarfin magoya bayan jam’iyyar tun daga matakin ƙasa.
Mataimakin Gwamnan ya buƙaci mahalarta taron su ɗauki wannan aiki da muhimmanci, yana mai cewa nasarar shirin zai dogara ne kan jajircewarsu, gaskiya da kuma sadaukarwarsu.
Mani Malam Mummuni ya ƙara da cewa wannan shiri ba wai don yin rijistar ’yan jam’iyya kaɗai ba ne, har ma don ƙarfafa tsarin jam’iyyar a matakin ƙasa da kuma gina hadaddiyar dandali da zai ci gaba da wakiltar muradu da burin al’ummar Jihar Zamfara.
Haka kuma, a madadin Gwamnan Jihar, Dakta Dauda Lawal, Mataimakin Gwamnan ya yi wa mahalarta taron fatan samun muhawara mai amfani da kuma nasarar gudanar da taron.
Mataimakin Gwamnan ya yi rijistar ne tare da wasu mambobin Majalisar Zartarwa ta Jihar.
COV / AMINU DALHATU
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
