Ilimi
Kano Ta Kaddamar da Kwamitin Jagoranci Don Shirin Tarayyar Turai na Ilimi da Ƙarfafa Matasa
Daga Khadijah Aliyu
Gwamnatin Jihar Kano ta kaddamar da Kwamitin Jagorancin Shirin Ilimi da Ƙarfafa Matasa a Arewa maso Yammacin Najeriya (EYEPINN) wanda kungiyar Tarayyar Turai ke daukar nauyinsa domin fadada damar samun ingantaccen ilimi da kuma karfafa gwiwar matasa a yankin.
An gudanar da bikin kaddamarwar ne a Kano, karkashin jagorancin Kwamishinan Ilimi na Jihar, Dakta Ali Haruna Abubakar Makoda.
Yayin jawabinsa, Dakta Makoda ya bayyana shirin EYEPINN a matsayin “Alƙawari mai Manufa”, yana mai cewa manufar shirin ita ce cike gibi a fannin ilimi, karfafa haɗin kai, da kuma baiwa matasa kwarewar da ta dace domin rage yawan yaran da ba sa zuwa makaranta a jihar.
Ya ce sabon kwamitin da aka kaddamar zai yi jagoranci kan dabaru, tsare-tsare, kulawa da tabbatar da gaskiya da inganci wajen aiwatar da ayyukan EYEPINN a fadin Kano.
Dakta Makoda ya kara da cewa, mambobin kwamitin sun haɗa da wakilai daga ma’aikatun gwamnati, hukumomi da cibiyoyi masu ruwa da tsaki, abokan hulɗa, da kuma wakilan Tarayyar Turai.
A yayin taron, abokan hulɗa ciki har da UNICEF, PLAN International, UNESCO, da kuma sashen nazari na ci gaban duniya (DIME) na Bankin Duniya, sun gabatar da jawabai da suka fayyace manufofi, da sakamakon da ake sa ran samu, da tsarin haɗin gwiwa, domin ƙarfafa tsarin samar da ilimi da kuma ƙarfafa matasa a Kano da ma yankin Arewa maso Yamma baki daya.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
-
Labarai4 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
