Connect with us

Labarai

‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 27 A Jihar Katsina

Published

on

‘Yan bindiga sun kutsa garin Unguwar Mantau a karamar hukumar Malumfashi ta jihar Katsina, inda suka kashe akalla mutane 27, suka jikkata wasu da dama tare da yin garkuwa da kimanin 15.

Maharan dauke da bindigogi kirar AK-47 sun isa kauyen da Asubahin fari a kan babura, inda suka fara kai hari a wani masallaci, sukayi harbin mai kan uwa da wabi, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 16  nan take.

Shaidu sun ce daga baya maharan sun shiga unguwannin kauyen, inda suka kashe karin mutane 11 tare da yin garkuwa da mata da dama ciki har da masu shayarwa.

‘Yan bindigar sun kuma lalata gidaje, shaguna da motocin al’umma yayin harin.

Unguwar Mantau tana da tazarar kilomita 17 daga garin Malumfashi.

Gwamnatin Katsina ta tabbatar da harin, amma ta ce adadin mutanen da aka kashe bai kai ba. Kwamishinan tsaron cikin gida, Muazu Danmusa, ya ce mutum 13 ne aka kashe, sai dai mazauna kauyen sun dage cewa sun binne gawarwaki 27.

Wani mazaunin garin mai suna Inusa Ladan ya ce: “Mun yi jana’izar wadanda aka kashe, gawarwaki 27 muka kirga.

Gwamnatin ta bayyana cewa harin ramuwar gayya ne, domin a baya mutanen kauyen sun yi kwanton bauna ga ‘yan bindiga suka kashe da dama daga cikinsu.

A fusace, mazauna Karfi da wasu kauyuka sun toshe hanyar Malumfashi zuwa Funtua, inda suka yi tattaki mai nisan kilomita 10 zuwa Malumfashi don nuna rashin jin dadinsu.

Daga bisani jami’an tsaro sun tarwatsa masu zanga-zangar, tare da bada tabbacin cewa za a kamo maharan domin hukunta su.

Karamar hukumar Malumfashi na fama da hare-haren ‘yan bindiga a ‘yan makonnin nan. ‘Yan bindiga sun kai hari Gidan Maijimina, Gidan Barau da Gidan Hazo, inda suka kashe mutane, suka kuma yi garkuwa da wasu tare da sace dabbobi da kayayyaki.

Yawaitar hare-haren ya tilasta al’ummomi da dama a kudancin Katsina neman sulhu da ‘yan bindiga domin su tsira.

A watan Yuli, kauyuka da suka hada da Gidan Maijimina, Unguwar Gishiri, Koro da Gidan Dandaudu sun hada Naira miliyan 15 wanda suka bai wa ‘yan bindiga domin  samun damar yin noma.

Mazauna kauyukan sun koka cewa gwamnati ta barsu cikin halin kaka-ni-ka-yi “Muna da zabin biyu ne kawai: ko mu yi sulhu da su ko mu gudu,” in ji Malam Ado Karfi wanda aka yi garkuwa da mahaifinsa sau biyu.

Ya kara da cewa ya sayar da gonaki biyu domin biyan kudin fansa har naira miliyan 3.5 cikin shekaru biyu.

Daga Isma’il Adamu

Labarai

Labarai6 hours ago

Hukumar Kula da Kogin Benuwe ta Dauki Matakin Yashe Laka da Yashi da ke Barazana ga Noman Rani

Ayyukan ban ruwa a yankin Kogin Benuwe na fuskantar barazana sakamakon taruwar Laka da Yashi a kogin, lamarin da ke...

Labarai1 day ago

Gwamna Namadi Ya Raba Tallafin Ramadan ga Ma’aikata da Marasa Galihu

Daga Usman Muhammad Zaria Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya raba tallafin kayan abinci na watan Ramadan tare da...

Labarai1 day ago

Sojoji Sun Yi Nasarar Kwato Dabbobi 257 da Aka Sace a Karamar Hukumar Gwarzo

Daga Abdullahi Jalaluddeen Sojojin Najeriya sun sami nasarar dawo da Shanu da Awaki  257 da aka sata a  wani aikin...

Labarai1 day ago

Uwargidan Gwamnan Zamfara ta Yaba da Yadda Aka yi Rabon Tallafin Ramadan

Daga Aminu Dalhatu  Uwargidan Gwamnan Jihar Zamfara, Hajiya Huriyya Dauda Lawal, ta yaba wa dukkan masu ruwa da tsaki bisa...

Labarai1 day ago

Gwamnatin Kebbi Za ta Raba Hatsi da Kayayyakin Aikin Gona ga Marasa Galihu

Daga Sani Dutsinma Gwamnatin Jihar Kebbi ta kammala shirye-shiryen raba kayayyakin aikin noma da nau’o’in hatsi daban-daban ga mutane miliyan...

Labarai1 day ago

Gwamnatin Kwara Ta Jaddada Kudurinta Na Kula Da Jin Daɗin Masu Harkar Sufuri

Gwamnatin Jihar Kwara ta bai wa masu harkar sufuri a jihar tabbacin ci gaba da kare muradunsu da jin daɗinsu....

Labarai1 day ago

Gwamnan Zamfara Ya Haramta Karbar Kudin Haraji A Hannu

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya bayar da umarnin dakatar da duk wani tsarin karbar kuɗaɗen shiga ta tsabar kuɗi...

Labarai1 day ago

Gwamnatin Tarayya Ta Faɗaɗa Rijistar Tallafin Jama’a Domin Tantance Masu Buƙata

Gwamnatin Tarayya na faɗaɗa tare da ƙarfafa Rijistar Tallafin Jama’a ta Ƙasa National Social Register domin tabbatar da cewa an...

Labarai1 day ago

Gwamna Idris Ya Ba da Umarnin Binciken Gobarar da Ta Tashi a Makarantar Nurul Haqq da ke Birnin Kebbi

Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya bayar da umarnin gaggauta kafa wani kwamitin bincike mai ƙarfi domin gano musabbabin gobarar...

Labarai1 day ago

Taraba Ta Kaddamar da Rarraba Kayan Aikin A Kananan Hukumomi 16

Hukumar Kula da Ci gaban Kiwon Lafiyar Matakin Farko ta Jihar Taraba ƙarƙashin Shirin IMPACT, ta ƙaddamar da rarraba kayan...

Mafi Shahara