Labarai
Gwamna Namadi Ya Tsige Rabi’u Kaugama Daga Mukaminsa
Gwamnan Jihar Jigawa, Umar Namadi, ya tsige Rabi’u Garba Kaugama daga mukaminsa na Mai Bai wa Gwamna Shawara kan Harkokin Majalisar Tarayya, nan take.
Wannan mataki an sanar da shi ne ga manema labarai cikin wata sanarwa da Sakataren Gwamnatin Jihar Jigawa, Malam Bala Ibrahim ya sanya wa hannu.
Sanarwar ta ce: “A sanadiyar wannan mataki, an dakatar da dukkan hakkoki da fa’idodi da suka shafi ofishinsa na Mai Bai wa Gwamna Shawara kan Harkokin Majalisar Tarayya.”
Bugu da ƙari, sanarwar ta umarci tsohon Mai Bai wa Gwamnan Shawara da ya mika dukkan kayan gwamnati da ke hannunsa ga ofishin Sakataren Gwamnatin Jihar Jigawa nan take.
Usman Muhammad Zaria
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai1 day ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai1 day ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
