Connect with us

Labarai

Kwastam ta Kama Kayayyaki na Sama da Naira Miliyan 478 a Jihar Kwara

Published

on

Daga Ali Muhammad Rabi’u 

Hukumar Kwastam ta Kasa reshen Jihar Kwara ta kama tare da kwace kayayyakin da aka haramta shigowa da su ko kuma aka takaita, da kudinsu ya haura Naira miliyan 478 a bana.

Mukaddashin shugaban hukumar  a yankin Jihar Kwara, Mataimakin Kwanturola Najeem Ogundeyi ne ya bayyana hakan yayin zantawarsa da manema labarai kan ayyukan hukumar a jihae .

Ya ce hukumar ta kuma samar wa gwamnati kudaden shiga da suka kai sama da Naira biliyan 2 da miliyan 500, wanda hakan ke nuna irin gudunmawar da take bayarwa wajen tallafawa manufofin tattalin arzikin gwamnati.

A cewarsa, hukumar na da kudurin kare tattalin arzikin kasa tare da tabbatar da bin doka da oda.

Ogundeyi ya kara da cewa hukumar za ta tabbatar da cewa jihar ba ta zama mafakar masu safarar haramtattun kayayyaki ba, yana mai gargadin cewa duk wanda ya yi yunkurin tauye tattalin arzikin kasa ta hanyar fasa kwauri zai fuskanci hukunci mai tsauri.

Ya bayyana cewa duk da gargadi da ake yi akai-akai, har yanzu ana ci gaba da safarar kaya ta barauniyar hanya, musamman shigo da shinkafa daga kasashen waje ba bisa ka’ida ba, lamarin da ke barazana ga manoman gida da kuma samar da abinci a kasa.

Ogundeyi ya ce haramta shigo da irin wannan shinkafa wata muhimmiyar dabara ce ta karfafa gwiwar manoma na cikin gida, samar da ayyukan yi, da kuma wadata kasa da abinci.

Ya kara jaddada cewa wadannan nasarorin da aka samu sun samo asali ne daga sahihan bayanan sirri da kuma hadin gwiwa da sauran hukumomin tsaro.

Ya kuma yi kira ga mazauna yankunan kan iyaka, ‘yan kasuwa da daukacin jama’a da su hada kai da hukumar domin kare masana’antun cikin gida, kiyaye tattalin arzikin kasa, da kuma bunkasa ci gaba mai dorewa.

Daga cikin kayayyakin da rundunar ta kama sun hada da motoci guda biyar, buhuna 1,107 na shinkafar  waje, buhuna 44 na sukari da aka shigo da su daga kasashen waje, jarkoki 317 na man fetur (PMS), buhuna 120 na ma’adinin lithium da aka hako ba bisa ka’ida ba, da kuma daruruwan kayan sawa wato gwanjo,  da kayayyakin gyaran motoci.

Labarai

Labarai18 hours ago

Tinubu Ya Nada Lamido Yuguda Mataimakin Gwamnan Babban Bankin Kasa

Daga Bello Wakili Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya nada Lamido Abubakar Yuguda a matsayin Mataimakin Gwamnan Babban Bankin Kasa CBN,...

Labarai19 hours ago

An Nada Kabir Yahaya Darakta Janar na Farko na Filin Jirgin Sama da ke Gusau

Daga Aminu Dalhatu Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya amince da naɗin Kabir Yahaya Gusau a matsayin Darakta Janar na...

Labarai20 hours ago

Kwastam ta Kama Kayayyaki na Sama da Naira Miliyan 478 a Jihar Kwara

Daga Ali Muhammad Rabi’u  Hukumar Kwastam ta Kasa reshen Jihar Kwara ta kama tare da kwace kayayyakin da aka haramta...

Labarai2 days ago

NEMA Da Masu Ruwa Da Tsaki Sun Kara Haɗa Gwiwa Don Hana Aukuwar Ambaliya Da Hadarin Tankar Mai

  By Adamu Yusuf   Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA), tare da haɗin gwiwar masu ruwa da...

Labarai3 days ago

Kaduna Ta Kaddamarda Shirin Rabon Maganin Kariya Daga Cutar Dundumi

  Daga Khadija Kubau   Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Kaduna tareda haɗin gwiwar kungiyar Sightsavers sun kaddamar da shirin raba...

Ilimi3 days ago

Hukumar Ilimantar Da Makiyaya Ta Kasa Ta Horarda Ma’aikatanta Kan Yanda Za’a Mayarda ‘Ya’yan Makiyaya Makaranta 

  By Adamu Yusuf   Hukumar Ilimantar da Makiyaya Ta Kasa (NCNE) ta shirya taron horas da ma’aikatan ta kan...

Labarai3 days ago

NCAA ta Yaba wa Hukumar Alhazai ta Jihar Kebbi Bisa Kyakkyawan Tanadin Aikin Hajji

Daga Sani Dutsinma Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta Najeriya (NCAA), ta yaba da kokarin Hukumar Jin Daɗin Alhazai...

Labarai3 days ago

Sojoji Sun Kashe ’Yan Bindiga 45 a Katsina

Rundunar sojin Najeriya ta kashe ’yan bindiga 45 a wani mummunan artabu da aka yi a yankin Danmusa na cikin...

Labarai3 days ago

Gwamnatin Kebbi Ta Bukaci Malamai Su Yi Wa’azin Zaman Lafiya

Gwamnatin Jihar Kebbi ta karyata zargin cewa gwamnatin Gwamna Nasir Idris ba ta taka rawar gani wajen bunkasa harkokin addinin...

Labarai3 days ago

Ranar Mata Ta Duniya: Gwamnatin Kano Ta Bukaci A Kara Tallafa wa Mata da ’Yan Mata

Kwamishinar Harkokin Mata, Yara da Masu Bukata ta Musamman ta Jihar Kano, Amina Abdullahi, ta bukaci masu ruwa da tsaki...

Mafi Shahara