Labarai
An Bukaci Kiristocin Kwara Su Taimaki Wasu a Sabuwar Shekara
An yi kira ga Kiristoci a jihar Kwara da su yi amfani da ni’imomin da Allah Ya hore musu wajen inganta rayuwar sauran al’umma, musamman masu bukata, a wannan sabuwar shekara.
Bishop na Cocin Anglican, Right Reverend Sunday Adewole, ne ya yi wannan kira a cikin sakon sabuwar shekararsa da ya gabatar wa mabiya a cocin St. Barnabas Cathedral da ke Ilorin.
Ya ce akwai matuƙar buƙatar masu hali su tallafa wa marasa galihu domin faranta musu rai da rage musu wahalhalu.
A cewarsa, idan lokaci ya yi na zuwa wurin aiki, bai dace mutum ya kasance yana coci yana ibada ba, domin kowane abu yana da lokacinsa.
Bishop Adewole ya jaddada cewa lokaci ya yi da ya kamata kowa ya ɗauki aikinsa da muhimmanci sosai, tare da guje wa sakaci da lalaci a harkokin kasuwanci ko aiki.
Ya ƙara da cewa ya dace a ba kowane abu muhimmancin da ya dace da shi, yana mai cewa duk wanda ke neman wadata da ci gaba, ya nemi taimakon Allah ta hanyar roƙon Ubangiji.
Bishop Adewole ya kuma shawarci mabiya da su nuna ƙauna da himma a aikinsu, su saita manufofi domin tabbatar da ci gaba da bunƙasa rayuwa a wannan sabuwar shekara.
Limamin ya ƙara da kiran da ya yi musu na ci gaba da kasancewa masu yawan addu’a, tare da sadaukar da kansu ga karatun Littafi Mai Tsarki a kowane lokaci, domin samun nasara a rayuwarsu.
Haka kuma ya gargade su da su kasance masu gamsuwa da abin da suke da shi, tare da ladabi da bin doka, domin hakan ne zai taimaka musu wajen cimma burinsu a rayuwa
Ali Muhammad Rabiu
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai21 hours ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai23 hours ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
