Labarai
An Bukaci Kafafen Watsa Labarai Su Riƙa Kiyaye Ƙa’idojin Aikin Jarida
An yi kira ga ƙwararrun ma’aikatan kafafen watsa labarai da su riƙa kiyaye ƙa’idojin aikin jarida tare da tabbatar da sahihanci da daidaito wajen ruwaito abubuwan da ke faruwa.
Gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ne ya yi wannan kira a cikin sakonsa yayin bikin kaddamar da gidan rediyon Emirate FM 98.5 Ilorin da aka gudanar a Ilorin.
Gwamnan, wanda Kwamishiniyar Sadarwa ta jihar, Hajiya Bolanle Olukoju, ta wakilta, ya bayyana kafa gidan rediyon a matsayin abin a yaba da kuma alheri ga ci gaban jihar.
A cewarsa, gwamnatin jihar za ta ci gaba da samar da yanayi mai kyau da zai bai wa harkokin kasuwanci masu zaman kansu damar bunƙasa da haɓaka.
Gwamna AbdulRazaq ya shawarci ’yan jarida da su guji duk wani aiki da ka iya kawo cikas ko tauye tsaro a jihar da ma ƙasar nan baki ɗaya.
Da yake nasa jawabin, Babban Mai Kula da Ƙungiyar Muslim Media Watch Group of Nigeria, Alhaji Ibrahim Abdullahi, ya bayyana taron a matsayin wani muhimmin mataki da ya dace a yi koyi da shi.
Ya ce kafa gidan rediyon ya ƙara yawan hanyoyin isar da sahihan bayanai a jihar Kwara.
Alhaji Abdullahi ya kuma ja hankalin ma’aikatan gidan rediyon da su guji watsa labaran ƙarya, tare da nisantar duk wani abu da zai iya ɓata sunan jihar da ƙasar nan.
Ya ƙara da cewa ya dace masu gidan rediyon su yi amfani da kafar wajen kare muradun bil’adama da inganta walwalar al’umma.
A nasa ɓangaren, wanda ya kafa Emirate FM 98.5 Ilorin, Malam Abdulazeez Arowona, ya ce sha’awarsa da ƙaunarsa ga aikin jarida ne suka ba shi ƙwarin gwiwar kafa wannan gidan rediyo.
Ya tabbatar da aniyarsa ta amfani da kafar wajen yi wa al’umma hidima, tare da bayar da gudummawa wajen bunƙasa ci gaba da raya jihar Kwara.
Ali Muhammad Rabiu
-
Labarai4 days agoHukumar Alhazai Ta Jigawa Ta Bayyana Alhininta Bisa Rasuwar Suleiman Usman
-
Fasaha3 days agoNASENI Ta Ƙarfafa Horar da Sana’o’i da Fasahar Jiragen Sama Marasa Matuki a Kaduna
-
Labarai3 days agoNSCDC Ta Kama Wanda Ake Zargi Da Safarar Mutane A Zamfara
-
Labarai2 days agoGwamnatin Tarayya Ta Ɗauki Matakan Gaggawa Bayan Tabbatar da Ebola a Birnin Tarayya
-
Labarai2 days agoGwamna Uba Sani Ya Ce Bunƙasa Ƙwarewa Na Da Muhimmanci Ga Farfaɗo Da Tattalin Arziki
-
Labarai2 days agoGwamnatin Zamfara Ta Nuna Damuwa Kan Ƙaruwar Hare-Haren ’Yan Bindiga
-
Labarai2 days ago’Yan Sanda Sun Kama Wanda Ake Zargi da Fashi da Makami A Kano
-
Labarai2 days agoTajudeen Zai Bayyana Rahoton Ayyukan Tinubu Cikin Kwanaki 14
