Labarai
Jami’ar Bayero Kano Ta Yi Martani Kan Zargin Damfarar Dalibi
Jami’ar Bayero Kano (BUK) ta yi martani kan zarge-zargen da ke yawo cewa wani mutum da ake zargin yana ikirarin kasancewa dalibin jami’ar yana aikata damfara ta yanar gizo tare da yin amfani da sunan wani.
A wata sanarwa da Daraktan Harkokin Hulɗa da Jama’a na jami’ar, Lamara Garba, ya fitar, jami’ar ta jaddada cewa tana da tsauraran ƙa’idoji kan halayya, ladabi da kuma ɗabi’ar da ake bukata daga dukkan dalibanta.
Jami’ar ta kuma bayyana cewa duk wani abu da wani dalibi ya aikata ba lallai ba ne ya wakilci dabi’u da martabar jami’ar gaba ɗaya.
Sanarwar ta ce bayan bullar zargin, jami’ar ta fara bincike na farko domin gano gaskiyar lamarin, inda hukumomin jami’ar ke duba batun bisa ƙa’idojin gudanarwa da hanyoyin ladabtarwa da aka tanada.
Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya bayyana ne bayan Farfesa Farooq Kperogi, malamin sadarwa ta zamani a wata jami’a da ke Amurka, ya bayyana a fili cewa wani da ake zargi da damfara yana ikirarin dalibi ne na BUK yana neman taimakon kuɗi tsawon shekaru domin biyan kuɗin makaranta.
Malamin ya gano cewa mutumin yana amfani da sunan ƙarya ne, har ma yana kwaikwayon mace domin samun kuɗi. Bayan wallafar bayanin Farfesa Kperogi, wasu mutane ma sun fito suna cewa su ma sun fuskanci irin wannan damfara.
Jami’ar ta yaba da ƙoƙarin Farfesa Kperogi da sauran mutane masu taimaka wa dalibai mabukata ta hanyar tallafa musu da kuɗin rajista da sauran bukatun karatu, tana mai cewa irin wannan taimako na taimakawa wajen faɗaɗa damar samun ilimi.
Jami’ar ta kuma tabbatar wa jama’a cewa idan bincike ya tabbatar da zargin, za a ɗauki matakin ladabtarwa da ya dace bisa dokokin jami’ar da kuma dokokin ƙasa.
Har ila yau, jami’ar ta bukaci jama’a da su bar binciken ya kammala cikin natsuwa tare da kauce wa yaɗa bayanan da ba a tabbatar da sahihancinsu ba.
Rel / Khadijah Aliyu
-
Labarai7 days agoSojojin Najeriya Sun Karɓi Motocin Yakin Da Aka Kera A Cikin Ƙasa
-
Labarai7 days agoKaramar Hukumar Birnin Kudu ta Nemi Hadin Kan Kungiyar ‘Yan Achaba Wajen Dakile Matsalar Tsaro
-
Labarai4 days agoRanar Mata Ta Duniya: Gwamnatin Kano Ta Bukaci A Kara Tallafa wa Mata da ’Yan Mata
-
Labarai7 days agoMajalisar Dokokin Jihar Kano Ta Fara Shari’ar Tsige Mataimakin Gwamna Aminu Abdulsalam
-
Labarai7 days agoRamadan: Tinubu Ya Kara Jaddada Kudirinsa na Inganta Rayuwar Jami’an Soji
-
Labarai4 days agoGwamnatin Kebbi Ta Bukaci Malamai Su Yi Wa’azin Zaman Lafiya
-
Labarai7 days agoTsarin Kundin Shirin Bunkasa Samarda Abinci Mai Gina Jiki
-
Labarai4 days agoSojoji Sun Kashe ’Yan Bindiga 45 a Katsina
