Labarai
BUK Ta Haramta “Signing-Out” A Harabar Jami’ar
Mahukuntan jami’ar Bayero Kano sun sanar da haramta duk wasu bukukuwan “signing-out” da kuma amfani da rigunan kammala karatu ba tare da izini ba a harabar jami’ar.
A cikin wata sanarwa da Daraktan Harkokin Jama’a, Lamara Garba, ya sanya wa hannu a madadin Magatakardan jami’ar ta bayyana damuwarta kan yadda ake samun karuwar bukukuwan “signing-out” da daliban da ke shirin kammala karatu ke yi.
Sanarwar ta ce daga yanzu an haramta duk wani nau’i na wadannan bukukuwa. Hakan ya hada da sanya tufafin da aka lalata ko aka rubuta a jikinsu, amfani da fenti, tawada ko alamar rubutu a jiki ko a kadarorin jami’a, tayar da tarzoma ko hayaniya a bainar jama’a, da duk wasu ayyuka makamantan haka da ake yi da sunan murnar kammala karatu.
Haka kuma, mahukuntan jami’ar sun hana daliban da ke shirin kammala karatu amfani da rigunan kammala karatu (academic gowns) ko wasu tufafi na musamman domin daukar hotuna ko gudanar da bukukuwa ba bisa ka’ida ba a cikin harabar jami’a. Sun jaddada cewa rigunan kammala karatu an tanade su ne kawai domin bukukuwan da jami’a ta amince da su a hukumance.
Sanarwar ta yi gargadin cewa duk wani dalibi ko gungun dalibai da aka samu suna aikata irin wadannan abubuwa za a hukunta su bisa tanadin dokoki da ka’idojin jami’ar.
Jami’ar ta kuma tunatar da dalibai cewa bayar da shaidar digiri ba ya ta’allaka ga nasarar karatu kadai ba, har ma da kyawawan halaye da da’a. Don haka, an bukaci daliban da ke kammala karatu su nuna hali da ɗabi’ar da za su kare mutunci da martabar jami’ar.
Haka zalika, an umarci jami’an tsaro su tabbatar da cikakken bin wannan umarni tare da kama duk wanda ya karya dokar.
Jami’ar ta shawarci dukkan dalibai da su yi biyayya da wannan umarni yadda ya kamata.
Khadijah Aliyu/Kano
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
