Ilimi
NELFUND Ya Raba Sama da Naira Biliyan 3 ga Daliban BUK
Daga Khadijah Aliyu
Asusun Bada Lamunin Ilimi na Najeriya (NELFUND) ya raba jimillar Naira Biliyan 3 da Miliyan 39 a matsayin kudaden karatu ga daliban Jami’ar Bayero da ke Kano su 27,640, a wani mataki na fadada damar samun ilimi cikin sauki.
Shugaban Jami’ar, Haruna Musa ne ya bayyana hakan yayin wata ziyarar girmamawa da Darakta Janar na NELFUND, Akintunde Sawyerr, tare da tawagarsa suka kai jami’ar.
Ziyarar, na da nufin karfafa hadin gwiwa tsakanin bangarorin biyu da kuma tattauna batutuwan da suka shafi kudaden da ke bai wa dalibai.
A jawabinsa, Farfesa Haruna Musa ya yaba wa NELFUND kan irin tasirinsa ga dalibai, yana mai cewa shirin ya taimaka matuka wajen kara damar shiga makarantu ga dimbin ‘yan Najeriya da ba za su iya yin rajista ba a baya.
Ya ce a zangon karatu na shekarar 2023/2024, daliba BUK 113 ne suka ci gajiyar shirin, inda aka biya Naira Biliyan 1 da Miliyan 494 a matsayin kudaden karatu.
Ya kara da cewa adadin ya karu sosai a zangon 2024/2025 zuwa dalibai 14,539, wanda kudaden suka kai jimillar Naira Biliyan 1 da Miliyan 545.
“Gaba daya, jimillar dalibai 27,640 daga Jami’ar Bayero sun amfana da shirin NELFUND, inda kudaden makaranta suka kai Naira Biliyan 3 da Miliyan 39, baya ga kudaden amfanin yau da kullum da ake biya kai tsaye ga daliban,” in ji shi.
Sai dai Shugaban Jami’ar ya bayyana cewa wasu dalibai sun fuskanci matsaloli yayin neman lamunin da kuma karbar kudade ta shafin NELFUND. Inda ya bayyana fatan tawagar za ta zage damtse wajen tabbatar da magance wadannan matsaloli.
Tun da farko, Mista Sawyerr ya ce ziyarar na da nufin kara zurfafa hadin gwiwa ne da jami’ar, yana mai tabbatar da cewa za a duba korafe-korafen dalibai domin saukaka tsarin neman lamunin da sake nema.
Haka kuma ya shawarci jami’ar da ta rika bude shafinta a kan lokaci domin bai wa dalibai damar yin rajista da wuri, tare da samun kudaden amfanin yau da kullum ba tare da jinkiri ba.
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai21 hours ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai23 hours ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
