Labarai
Majalisar Dokokin Jihar Zamfara ta Dakatar da Shugabannin Kananan Hukumomi Biyu
Daga Aminu Dalhatu
Majalisar Dokokin Jihar Zamfara ta dakatar da shugabannin kananan hukumomi biyu bisa zargin rashin rikon amana da gaskiya wajen tafiyar da kudaden jama’a, bayan tattaunawa a zaman majalisar da aka gudanar a yau.
Shugaban Majalisar, Bilyaminu Ismail Moriki ne ya jagoranci zaman, inda aka mayar da hankali kan inganta gaskiya da rikon amana wajen tafiyar da kudaden jama’a a matakin kananan hukumomi.
Matakin ya biyo bayan gabatar da rahoton Kwamitin Majalisar kan Kananan Hukumomi da Harkokin Sarauta, wanda Mataimakin Shugaban Majalisar, Adamu Aliyu Gummi, ya gabatar.
Rahoton na daga cikin binciken da ake yi kan yadda aka tafiyar da harkokin kudi na kananan hukumomi 14 na jihar a shekarar kasafin kudi ta 2025.
A cewar kwamitin, shugabannin da abin ya shafa su ne Mannir Mu’azu Haidara na karamar hukumar Kaura Namoda da kuma Umar A. Faru na karamar hukumar Bukkuyum, bisa zargin kin amsa gayyatar da aka yi musu domin bayyana yadda aka kashe kudaden da aka ware wa kananan hukumominsu.
Bayan tattaunawa, majalisar ta amince baki daya da dakatar da su har sai an kammala binciken.
An kuma umarci shugabannin biyu da su mika ragamar tafiyar da kananan hukumominsu ga mataimakansu nan take.
Majalisar ta ce daukar wannan mataki ya zama wajibi sakamakon abin da ta bayyana a matsayin rashin girmamawa ga majalisar, da kuma rashin gaskiya da rikon amana wajen tafiyar da harkokin kananan hukumomin nasu.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai7 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai7 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Labarai7 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai7 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
